Yakin Syria: Dakarun Syria sun kashe sojojin Turkiyya 29 a Idlib

Turkish troops in north-western Syria. File photo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dakarun Turkiyya na mara wa 'yan tawaye ne a Idlib na Syria
An wallafa

Rahotanni daga Syria na cewa jiragen yakin gwamnatin Bashar al Assad na Syria sun kashe a kalla sojojin Turkiyya 29 a yankin arewa maso yammacin kasar.

Rahmi Dogan Gwamnan lardin Hatay na Turkiyya ya ce an raunata wasiu sojojin na Turkiyya a yankin Idlib, Amma wasu rahotannin sun ce wadanda suka mutun sun zarce alkaluman da aka bayyana.

A halin yanzu, Turkiyya ta fara mayar da martani kan dakarun gwamnatin Syria.

Sojojin Syria na yunkurin kwato yankin na Idlib daga hannun 'yan tawaye tare da goyon bayan Rasha.

Kawo yanzu gwanatin Syria ba ta ce uffan ba kan lamarin da ya kawo karuwar rikici a yankin na Idlib, lardi na karshe da ke hannun masu adawa da gwamantin ta Syria.

Bayn Shugaba erdogan na Turkiyya ya kira wani taron gaggawa a birnin Ankara ne aka ga sojojin Turkiyyar sun fara kai hare-hare kan dakarun na Syria.

Map showing control of north-western Syria (24 February 2020)
Presentational white space

Shugaban na Turkiyya ya bukaci sojojin Syria su janye daga wuraren da suke rike da su kusa da wasu sansanonin da Turkiyyar ta kafa, kuma ya ce zai kai mu su hari idan ba su daina kutsawa cikin lardin ba.

Amma gwamnatin Syria da ta Rasha sun yi watsi da bukatun na Shugaba Erdogan.

Wata kungiya mai sa ido kan rikicin na Syria, Syrian Observatory for Human Rights, ta ce a kalla sojojin Turkiyya 34 aka kashe a harin na yammacin Alhamis.

An kuma tafi da wadanda suka sami raunuka zuwa Turkiyya domin shan magani.

Meanwhile, Nato-member Turkey said Foreign Minister Mevlut Cavusoglu had spoken to Nato Secretary-General Jens Stoltenberg.

Turkey-backed Syrian fighters ride on a tank in the town of Saraqeb, Syria's Idlib province. Photo: 27 February 2020

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Mayaka kum 'yan tawayen Syria da Turkiyya ke mara wa baya a Idlib