Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kauyen da cutar tundurmi ta yi wa katutu a Uganda
- Marubuci, Daga Patience Atuhaire
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kamwenge
- An wallafa
Duk da kasancewar tana zaune tana gyara wake a kofar gidanta, kafafun Margaret Tindimutuma a kumbure suke suna kuma yi mata ciwo.
Matar 'yan kasar Uganda mai fada a ji ce, amma kuma tana da wani irin ciwon tundurmi wanda ya sha bamban da sauran abin da yasa iyalanta ke ta fama da ita.
"A ko da yaushe na kan samu wani sauyi a jikina musamman idan na ci wani abu a lokacin ina karama".
Ta ce daga baya sai kafafunta suka fara kumbura da kuma ciwo.
Margaret Tindimutuma, ta ce idan suna ciwo sai ta rasa abin da ke mata dadi, wani lokaci har fita take kofar gida ta shimfida tabarma ta zauna don ta samu dan sauki.
Ta ce "A hankali radadin ciwon na karuwa, sai na fara ji kafafuna na farfashewa, fatar da ke tsakanin yatsuna ta fara fashewa, daga nan sai 'ya'yana biyu maza suka fara rashin lafiya",
"Na zaci ko su ma sun gaji ciwon ne".
Manyan 'ya'yanta biyu sun mutu sakamakon kumburin kafar da ciwo.
Ta ce sun zauna a kan wani benci a harabar gidansu a lokacin matar daya daga cikin 'ya'yanta da suka rasu Hope Amooti ta nuna musu hotunansu a lokacin da suke jin dadinsu.
Margaret Tindimutuma, ta ce "Dana dogo ne kyakkyawa ga fara'a, amma a lokacin da ciwo ya fara cin karfinsa duk sai kamanninsa suka sauya".
Matar marigayin cikin kuka ta ce "A lokacin da muke iya sayen maganin rage radadi ya kan dan tattaka, amma daga baya ko gadon da yake kwance ba ya iya bari".
Daya daga cikin 'ya'yan Mrs Tindimutuma mata wadda ta yi aure a wani kauye daban ita ma ta fara rashin lafiya, hannunta daya ya fara kumbura.
Daga nan sai ciwon ya koma kafafunta, kawai sai mijinta da 'yanuwansa suka fara tsanar ta har ta kai sun kore ta, ta tattara 'ya'yanta ta koma kauyensu Kyakatoma.
Mrs Tindimutuma ta ce, "Na saba nomawa iyalaina abinci mai yawan gaske da zai ishe mu tsawon lokaci, domin ba ma rasa abinci, amma a yanzu babu abinci a gidana".
Ta ce da nake muku magana yanzu, akwai wani makwabcinsu da ya kamu da irin wannan ciwo na tundurmi, domin har ta ci kafarsa sosai ga wari, saboda sabo ta ce har ta daina rufe hancinta ma.
A shekarar 2015, wata tawagar masana kimiyya suka ziyarci kauyen domin gano abin da ke janyo ciwon a kauyen, wanda Hukumar Lafiya Ta Duniya ta ce an fi samunsa a kasashen da suke da zafi.
Sun dauki samfurin kasar wajen, sannan suka yi wa masu ciwon wasu gwaje-gwaje.
Sakamakon masana kimiyyar ya nuna cewa nau'in cutar da ba kasafai ake samunsa ba wanda aka sani da suna podoconiosis shi ke damun mazauna kauyen wanda ke a lardin Kamwenge a yammacin Uganda.
To amma irin tundurmin da aka sani, shi tsutsotsi ne ke janyo shi ko sauro.
Kazalika kasar wajen ma na bayar da gudunmuwa wajen kamuwa da cutar tundurmi.
Wasu rahotonni sun nuna cewa akwai yiwuwar mutum 300 za su iya kamuwa da cutar a lardin Kamwenge kadai.
Akwai dai masu irin wannan nau'in cuta ta tundurmi a Habasha da Kamaru.
Hukumar Lafiya Ta Duniya ta kiyasta cewa akwai mutum kusan miliyan hudu da za su iya kamuwa da irin wannan nau'in cuta.
Bayan samun bayanai a game da wannan nau'in cuta, masana kimiyya sun shawarci mazauna kayen da su rinka sanya kayan kariya, sannan kuma su rinka wanke hannayensu da kafafunsu idan sun gama aiki a gona.
Bayan nan kuma su rinka sa takalmi idan za su fita daga gida.
Masana kimiyyar sun ce yin hakan zai taimaka wajen raguwar masu kamuwa da nau'in cutar tundurmi.
Wata da take dauke da wannan cuta, ta ce bayan ta wanke kafarta, ta kan zuba ruwa a babbar roba, sannan sai ta debi gishiri cikin cokalin cin abinci uku ta zuba a cikin ruwan, daga nan sai ta tsoma kafarta a ciki tsawon minti 15.
Ta ce "Idan na yi hakan sai na ji wani sauki da dadi a raina, har ma na fita hayyacina, to amma a wasu lokutan ba na samun kudin da zan sayi gishirin, sai ciwon ya dawo".
Wani likita a Uganda Dr Kihembo ya ce, akwai magungunan magance cutar tundurmin da ba nau'in podoconiosis ba, amma masu dauke da mai nau'in podoconiosis, su babu magani sai dai kawai su rinka shan maganin kashe radadi.