Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da suka faru a Najeriya a makon jiya
Kamar kowanne mako, a wannan makon da muke ban kwana da shi an samu manyan abubwan da suka fi jan hankalin jama'a a Najeriya.
Mun duba guda 10 daga ciki kamar haka:
An yi wa Buhari ihu a Maiduguri
Mutane a jihar Borno sun yi wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ihu a lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya jihar.
Bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta a kasar ya nuna yadda mutanen suka yi ta ihu suna cewa 'ba ma so, ba ma yi,' a daidai lokacin da ayarin motocin Buhari ke wucewa a kan titi.
Buhari ya je ta'aziyyar ne a fadar Shehun Borno, Abubakar Umar Garbai bayan harin da kungiyar Boko Haram ta kai wa matafiya a garin Auno a hanyar Maiduguri, inda suka kashe akalla mutum 30 tare da kona wasu a cikin motoci.
Harin Auno
Yadda Boko Haram suka kona mutane da ransu a Auno ya jawo suka ga shugaban, wanda ke halartar taron kungiyar tarayyar Afirka a Habasha, tare da zarginsa da gazawa wajen magance matsalar tsaro.
Zulum ya ba Buhari shawara kan Boko Haram
Da yake jawabi a fadar sarkin, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya shawarci Buhari da gwamnati ta sauya salonta na yaki da kuniyar Boko Haram.
Sannan ya bayyana damuwa game da sake dawowar hare-haren kungiyar, bayan an samu raguwarsa a watannin baya.
Kotun Koli
Kotun Kolin Najeriya ta soke zaben David Lyon na jami'iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya.
Hukuncin kotun ya biyo bayan samun mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo da laifin amfani da takardun boge wurin tsayawa takara.
Kotun ta soke kuri'un da jam'iyyar APC da 'yan takarar nata suka samu a zaben sannan ta bukaci hukumar zaben kasar INEC ta soke takardar shaidar cin zaben da ta ba su.
Ta kuma umarci hukumar zaben da ta ayyana wanda ya samu mafi yawan kuri'u a cikin sauran 'yan takarar a matsayin zababben gwamna.
Sabon gwamanan Bayelsa
Jam'iyyar PDP ta yi murna da hukuncin kotun, amma ta bukaci kotun ta sake nazari kan hukuncin zaben gwamnan Imo.
A nata bangare, jam'iyyar APC ta bakin shugabanta Adams Oshiomhole na ganin bai dace a ba wa PDP kujerar gwamnan Bayelsa ba.
Hukuncin Kotun Kolin ya fusata wasu da suka yi ta kone-kone a Yenagoa babban birnin jihar ta Bayelsa.
Dokar hana fita a Bayelsa
Sakamakon tashin tashinar da aka samu a babban birnin jihar Bayelsa, 'yan sanda sun sanya dokar hana fita ta kwana uku ana gab da rantsar da sabon gwamna Diri Douye.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Uche Anozia, ya ce an sanya dokar ta ranar Juma'a 14 ga watan Fabarairu ne saboda tashin hankali da aka samu a Yenagoa bayan INEC ta ba wa gwamnan takardar shaidar cin zabe.
Shekarar Sarkin Zazzau 45 a kan mulki
A makon da ya gabata ne aka sha shagalin bikin cikar Sarkin Zazzau Shehu Idris shekara 45 a kan mulki.
Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III da wasu sarakuna da manyan jam'ian gwamnati da attajirai da masoya sun halarci bikin tare mika sakon taya sarkin murna a lokacin kasaitaccen bikin.
Haka kuma an gudanar da hawan daba na musamman a fadar sarkin da ke birnin Zaria, inda mahayan dawaki da sarakai da sauran mabiyansa suka yi ta mika gaisuwa.
Su ma 'yan kallo sun halarta domin ganin yadda aka yi bikin cikar Sarkin shekara 45 a kan mulki.
Ranar Masoya
'Yan Najeriya sun bi sahu wajen bikin Ranar Masoya, inda masoya suka yi amfani da damar wajen tarairaya da kyutatawa tare da nuna kulawa ga juna.
Ranar 14 ga watan Fabarairun kowace shekara ce Ranar Masoya Ta Duniya, wato Valentine's Day.
An saki Agba Jalingo
Wata kotu a jihar Cross River da ke Najeriyra ta bayar da belin dan jaridar nan Agba Jalingo, wanda aka tsare na tsawon kwana 175 bisa zargin cin amanar kasa.
An kama Jalingo ranar 22 ga watan Agusta na 2019 bayan ya wallafa rahoton da ke zargin gwamnan jihar Ben Ayade da karkatar da naira miliyan 500 daga asusun jihar.
Tsare dan jaridar ya jawo suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da wasu 'yan kasar.
Sai dai mai shari'a Sule Shuaibu na babbar kotun tarayya da ke Calabar, ya bayar da belin Jalingo a kan naira miliyan 10 bayan lauyansa Attah Ochinke ya nemi yin hakan.
Kungiyoyin kare hakkin dan Adam irin su Amnesty International sun yi maraba da bayar da belin dan jaridar.
Sojoji sun karyata Amnesty
Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahoton Amnesty International, wanda ya zargi sojojin kasar da kona kauyuka a Borno.
Rundunar ta yi martanin ne a shafinta na Twitter inda ta ce dama Amnesty International ta saba bata wa sojin Najeriya suna.
Ta ce zarge-zargen da kungiyar ta yi yaudara ce kawai da kuma rashin sanin abubuwan da suke faruwa game da yakin da ake yi da masu tada kayar-baya a arewa maso gabashin kasar.
Kotu ta tsare 'yan fashin banki a Abuja
Wata kotu ta ba da umarnin tsare mutum biyar da ake zargi da fashi a wani bankin kasuwanci a Abuja a kurkukun Kuje sakamakon gurfanar da su a gaban kotu ranar Juma'a.
An tsare mutanen a rundunar 'yan sanda ta Abuja mako bakwai bayan sun aikata laifin da ake zarginsu.
Ana zarginsu da aikata laifuka biyar da suka shafi hada baki wajen yin fashi tare da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.
Lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen da ake yi musu, dukkan mutanen biyar sun musanta zargin.
Tattakin yaki da cin hanci
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci a Najeriya ta yi tattaki a fadin kasar domin wayar da kan jama'a game da illar cin hanci da rashawa.
EFCC ta ce ta ware ranar 14 ga watan Fabarairu, wato Ranar Masoya ta Duniya, domin gudanar da tattakin da niyyar janyo hankalin 'yan kasar bisa illar wannan mugunyar dabi'a.