'Yan gudun hijirar Kamaru na kwarara zuwa Najeriya'

An wallafa

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce dubban 'yan gudun hijira ne suka tsere daga Kamaru zuwa Najeriya.

Hukumar ta ce 'yan gudun hijira kimanin dubu takwas ne suka tsallaka Najeriya daga Kamaru cikin mako biyu.

Kuma ta ce wadanda suka ketara zuwa Najeriya sun shiga ne ta jihohin Taraba da kuma Cross Rivers, inda adadin 'yan gudun hijirar ya kai kimanin dubu sittin.

An samu kwararar 'yan gudun hijirar ne kafin zaben babban zaben da aka gudanar a Kamaru inda mutane suka tsere domin suna tsoron barkewar rikici tsakanin jami'an tsaro da masu dauke da makamai, a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.

Mataimakin wakilin Hukumar da ke lura da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya Roger Hollo ya ce 'yan gudun hijirar da suka isa kasar a yanzu haka an tsugunar da wasunsu ne a makarantu da asibitoci yayin da wasu kuma suka rabe a gidajen 'yan uwa da abokan arziki.

A cewarsa an yi rijistar 'yan gudun hijira dubu hamsin da daya kafin zuwan na baya-bayan nan a garuruwa fiye da dubu tamanin a jihohin Akwa Ibom da Benue da Cross River da kuma Taraba.

Ya kuma ce akwai kuma wasu da hukumar ta tsugunar da su inda ya ce suna samar musu da kariya da abinci da kuma magunguna.

A cewar Mista Roger Hollo hukumar tana aiki tare da hukumonin Najeriya don tabbatar da 'yan gudun hijirar sun samu muhimman abubuwan bukatun rayuwar yau da kullum.

Haka kuma ya ce abinci da wuraren kwana da magunguna su ne abubuwan da 'yan gudun hijira ke bukata cikin gaggawa, saboda makarantu ba za su iya daukar sabbin 'yan gudun hijirar da suke kwarara zuwa Najeriya ba.

Ya kuma ce akwai bukatar tallafa musu don su fara dogaro da kansu.

Bayanai na cewa 'yan gudun hijirar sun tserewa rikice-rikice ne wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu uku yayin da fiye da dubu dari shida da saba'in da tara suka rasa muhallansu, wasunsu ma sun ketaro zuwa Najeriya da munanan raunukan harbin bindiga.

Hukumar da ke lura da 'yan gudun hijira tana jagorantar kai daukin kasashen duniya don kare mutanen da aka tilastawa tserewa gidajensu saboda rikice-rikce da kuma musgunawa.