'Yan tawaye sun hana jiragen agaji na MDD tashi a Libya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mayakan Janar Khalifa Haftar sun kawo tarnaki ga yunkurinta na wanzar da zaman lafiya da samar da kayan agaji a Libya.

Ofishin MDD na Libya ya ce mayakan (LNA) na Khalifa Haftar sun hana jiragen Majalisar sauka da tashi a kasar.

A makonnin baya-bayan nan mayakan LNA sun sha haramata wa jiragen MDD izinin zirga-zirga a kasar.

''Ofishin MDD a Libya na takaicin yadda LNA ta hana zirga-zirgar jiragensa masu jigilar ma'aikata izinin sauka a Libya. An sha yin hakan a makonnin baya-bayan nan," in ji MDD.

Wani jami'in jin kai ya shaida wa AFP cewa Janar Haftar ya haramta tashin jirage a birnin Tripoli kuma akwai fargabar ana iya kai wa jiragen MDD hari.

Tun watan Afrilu mayakan LNA ke kokarin kwace iko da Tripoli daga gwamantin kasar ta GNA, wadda MDD ke goyon baya, amma ta kasa dakile hare-hare a birnin.

A hirar da BBC ta yi da shi a karshen mako, shugabann MDD António Guterres, ya ce rikcin Libya "abin kunya" ne.

Guterres ya zargi kasashe da ke da hannu a karya yarjejeniyar MDD kan sanya takunkumin sayar da makamai a Libya, inda ya ce hakan bai dace ba.