PDP ta yi wa Lai Mohammed martani kan gyaran NTA

Uche

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, PDP ta yi kira ga 'yan majalisa da kada su yarda a karbo bashin
An wallafa

Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta gargadi ministan yada labaran kasar, Lai Mohammed, da "kada ya sake ya saka Najeriya cikin kangin bashi".

Lai Mohammed ya bukaci 'yan majalisa su sahale masa karbo rancen dala miliyan 500, (kusan naira biliyan 181) domin tayar da komadar gidan talabijin na NTA, inda "zai mayar da shi kamar CNN na Amurka".

Kazalika PDP ta shawarci majalisar dokoki da ta ceci Najeriya ta hanyar kin amincewa da bukatar ministan, a cikin wata sanaarwa da ta fitar a daren Litinin.

Shi dai ministan ya ce za a karbo bashin ne daga cikin dala biliyan 29.96 da Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi majalisar ta sahale ya amso domin gudanar da manyan ayyuka a kasar.

'Yan Najeriya da dama ne suka sako ministan a gaba a shafukan sada zumunta kan kalaman nasa, inda ya zama na gaba-gaba cikin abubuwan da aka fi tattaunawa kansu a Twitter.

"PDP tana kira ga majalisar tarayya da ta dakile yunkurin wasu tsurari a fadar shugaban kasa da suke son kara lalata tattalin arzikin kasa," PDP ta bayyana a sanarwar.

Ta kara da cewa ta fahimci tun da Buhari ya hau mulki talauci ne kawai ya karu duk da bashin da ya rika karbowa.

Gwamnatin Buhari dai ta sha bayyana irin nasarorin da ta cimma na ayyukan kyautata rayuwar al'ummar Najeriya, ciki har da shirin nan na N-power da kuma ciyar da daliban makarantun firamare.