Zan mayar da NTA kamar CNN idan aka ba ni rancen ₦181b — Lai Mohammed

Lai Muhammad

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ministan watsa labaran Najeriya, Lai Mohammed, ya sha alwashin mayar da gidan talbijin din kasar, NTA, tamkar na Amurka CNN, idan majalisar dokokin kasar ta bari ya karbo rancen dala miliyan 500, kwatankwacin naira biliyan ₦181.

Kafofin watsa labaran Najeriya, ciki har da jaridar Guardian, sun rawaito cewa ministan ya bayyana haka ne lokacin da ya je gaban kwamitin kula da karbo bashi a ciki da wajen kasar na majalisar dattawa.

Ya kara da cewa yana so su amince a karbo bashin ne daga cikin $29.96b da Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi majalisar ta sahale ya amso domin gudanar da manyan ayyuka a kasar.

'Yan Najeriya da dama sun yi ta yi wa ministan shagube a shafukan sada zumunta, inda yanzu haka yake cikin manyan abubuwan da aka fi tattaunawa kansu a shafin Twitter.

Wani mai amfani da Twitter, Olusegun Iselaiye, ya ce ko da NTA za ta samu ninkin kudin da Lai Mohammed yake so a ranto, ba za ta zama tamkar gidan talbijin mai zaman kansa na kasar Channels TV ba, ballantana ma CNN.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shi kuwa Reno Omokri cewa ya yi babu wata bukatar da za ta sa Najeriya ta yi rancen $500m domin inganta NTA saboda a cewarsa, akwai bukatun da suka fi wannan.

"Da $500m za a iya gina sababbin makarantu 500 domin yara miliyan 13 da rabi da ba sa zuwa makaranta da kuma asibitoci 1,000 domin kula da kashi daya na mata da suke mutuwa sanadiyyar haihuwa," a cewarsa.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Ko a farkon watan Fabrairu, Lai Mohammed, ya yi wani jawabi da ya sa wasu 'yan Najeriya mayar da martani bayan ya karyata rahotannin da ke cewa majalisar dokokin kasar tana duba yiwuwar samar da wani kudiri da zai sa ido kan kafafen sada zumunta.

Wannan abu dai ya janyo ce-ce-ku-ce musamman a kafafen sada zumuntar inda wasu ke ganin a matsayinsa na ministan yada labarai, bai kamata a ce ya fito ya bayyana cewa bai ma san da kudirin ba sannan ba ya gaban zauren majalisa.

Daga bisani kuma ministan, cikin wata sanarwa ya fito ya bayyana cewa gwamnatin kasar za ta shirya wani taron masu ruwa da tsaki a watan nan na Fabarairu domin duba hanyoyin da za a bi wurin "tsaftace" yadda 'yan Najeriya ke amfani da shafukan sada zumunta.

Kalaman Lai Mohammed sun dade suna janyo ce-ce-ku-ce da muhawara a kasar musamman a shafukan sada zumunta.