Hanyoyi hudu da hana acaba zai shafi jama'ar Lagos

- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Tun bayan da gwamnatin Legas da ke Najeriya ta haramta yin acaba da babura masu kafa uku yin zirga-zirga a titunan jihar, al'umma ke kokawa sakamakon yadda suka tsinci kansu cikin karancin ababenn hawa wanda ya tilasta musu dabawa da kafarsu duk kuwa nisan wajen da za su.
Akasarin jama'ar jihar sun fi amfani da acaba, ko keke napep, wanda ake kira Marwa a birnin, wajen yin zirga-zirgarsu ta yau da kullum.
A watan jiya ne gwamnatin ta haramta amfani da acaba Opay da GOKADA da Maxkeke.
Gwamnatin jihar ta ce ta haramta masu baburan ne saboda karya doka da hadurran da masu sana'ar ke haddasawa.
A ranar Litinin ne wannan doka ta fara aiki gadan-gadan kuma da alamu fasinjoji da dama na daba sayyadarsu wajen kai kansu wuraren harkokinsu na yau da kullum.

BBC ta yi duba kan hanyoyi hudu da hana yin acabar da keke Napep za su shafi al'ummar jihar:
Jefa rayuwar dubban mutane cikin garari
Shu'aibu Idris Mikati, wani masanin tattalin arziki a jihar ta Legas, ya bayyana wa BBC cewa dokar za ta jefa rayuwar "sama da mutane 25,000 zuwa 50,000 da suka ta'allaka wajen yin amfani da okada wajen samun abinci" cikin mawuyacin hali.
Galibinsu sun dogara ne da wannan sana'a wajen ciyar da kansu da iyalinsu da kuma 'yan uwa da abokan arziki.
Ma'aikata da 'yan kasuwa masu karamin karfi da ke amfani da okada zuwa wajen harkokinsu na yau da kullum su ma za su fuskanci nakasu saboda da yawansu sun fi amfani da okada don zuwa wajen sana'oinsu, sakamakon cunkoson ababen hawa a kan titunan Legas.
Masu wadata za su tafka asara
A mafi yawan lokuta masu wadata ne ke sayen baburan okada ko keke napep domin bayar da haya ga wadanda za su gudanar da sana'ar su kuma rika ba su wani kaso daga cikin cinikin da suka yi a rana ko a wata - ya danganta da yadda suka kulla yarjejeniya tsakaninsu.
Sai dai wannan doka na iya sa mamallaka baburan okada ko keke napep su fuskanci koma baya musamman a kudaden shigarsu.
Yankunan da wannan doka ta shafa su ne wuraren da masu okada suka fi yin zirga-zirga kuma hakan zai sa su yi asarar kashi mai tsoka na kudaden da suke samu kowace rana.
Masu hannun jari za su ji jiki
Mafi yawan kamfanoni masu amfani da okada ko keke napep don saukaka sufuri a jihar sun ciyo bashin makudan kudade don gudanar da wannan kasuwancin wanda wannan doka za ta sa su cikin halin ni-'ya-su sakamakon matsalar da za su fuskanta ta rashin mayar da kudadensu.
A cewar Mikati, "akwai kamfanoni da yawa da suka ciyo bashi don dadadawa mazauna Legas don samun saukin hawa baburan".
"Akwai kamfanin da ya ciwo sama da bashin dala miliyan 15 wasu sama da dala miliyan 20" don su yi wannan sana'a, in ji shi.
Ya ce wannan doka za ta shafi irin wadannan kamfanoni mayuka.
Soke sana'ar ta okada da keke napep zai sa su durkushe tun da babu wadanda za su gudanar da sana'ar sakamakon haramcin da gwamnati ta yi.

Rasa ayyukan yi
Matsalar rashin aikin yi ce ta jefa miliyoyin mutane ga wannan sana'a ta okada ko keke napep wanda kuma wannan doka babbar barazana ce ta yadda masu wannan sana'a za su koma gidan jiya, ma'ana za su kasance ba su da sana'ar yi don ci da kansu da kuma iyalansu.
Su ma ma'aikata da ke aiki karkashin kamfanonin sufuri da ke amfani da okada za su rasa abin yi kuma hakan na iya jefa su cikin hadarin aikata miyagun laifuka a jihar, abin da gwamnati a kowane mataki a Najeriya take kokarin dakilewa.
Wannan batu na haramta okada da keke napep a jihar ta Legas ya janyo muhawara a kafafen sada zumunta musamman a Twitter inda tuni aka kirkiri maudu'ai biyu masu taken #OkadaBan da #KekeBan.
Ma'abota shafin na Twitter na ta bayyana ra'ayinsu game da sabuwar dokar da gwamnatin ta Legas ta bullo da ita, sai dai yayin da wasu ke koka wa kan yadda matakin zai shafi rayuwarsu ta yau da kullum, wasu kuwa suna maraba ne da matakin.
Ga dai wasu daga cikin ra'ayoyin ma'abota Twitter.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Matsalar acaba
Sai dai duk da irin kalubalen da ke tattare da wannan doka, masanin tattalin arzikin ya kuma bayyana wasu daga cikin matsalolin da irin wadannan baburan ke haddasawa a kan titunan jihar.
Ya ce "wasu daga cikin masu baburan na okada basa bin ka'idojin tuki musamman a yayin basu hannu kan danja".
"Suna ganganci akan hanya, ana samun hadari, mutane da yawa sun samu rauni musamman masu hawa baburan." a cewarsa.
Baya ga wadannan, Mikati ya bayyana cewa baburan kuma na bayar da gudummawa "wajen karuwar dumamar yanayi" ta yadda hayaki ke tashi daga baburan na okada.
Amma masanin ya ce gwamnatin Legas za ta samu alfanu da wannan mataki "saboda tana ganin ta siyo motocin sufuri wato bas-bas da zasu rika daukan talakawa daga lungu zuwa lungu a jihar, ta nan wajen gwamnatin za ta iya samun mutane da zasu shiga motocin sannan kuma ta samu kudaden shiga."