Abin da Buhari ya fada wa manyan hafsoshin tsaro

An wallafa

Fadar shugaban Najeriya ta musanta ikirarin da wasu 'yan kasar ke yi na cewa taron gaggawa da Shugaba Muhammadu Buhari ya kira a ranar Alhamis na da alaka da kiran wasu 'yan majalisar dattawa na neman shugaban kasar ya sauka daga mukaminsa saboda gaza shawo kan matsalolin tsaro.

Shugaban kasar ya gayyaci dukkanin manyan hafsoshin tsaro domin gudanar da taro, kwana guda bayan da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan kasar Sanata Eyinnaya Abaribe ya bukaci ya yi murabus saboda gaza cika alkawarin da ya yi na kiyaye rayuka da dukiyoyin al'ummar kasar.

Yayin wata hira da BBC, mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu, ya ce ko kadan taron ba shi da alaka da kalaman Sanata Abaribe.

"Hasalima taro ne da aka saba gudanarwa bisa al'ada, kuma tun kafin shi Sanatan yayi wadancan kalamai aka shirya taro," in ji Garba Shehu.

Ya ci gaba da cewa ''Mun dauka kalaman sun fito ne daga inda ya dace, Sanata Abaribe na gaban kotu a yanzu haka, shi ne ya fitar da Nnamdi Kanu wanda ke kokarin kafa kasar Biafra daga kurkuku, don haka 'yan Nigeria su san wanene shi, mu a wajen mu ba shi da hurumin yin wannan magana''.

Ya kuma karyata zargin da wasu ke yi na cewa gwamnatin shugaban kasar ta gaza shawo kan matsalolin tsaro a Najeriya.

"A yanzu matsalar ta shafi yawancin kasashen da ke yankin Sahel, don haka dukkanin wadannan kasashe na aiki tare don tabbatar da an samu nasarar yaki da laifukan ta'addanci," in ji Garba Shehu.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar Garba Shehu da Sani Aliyu na BBC: