Najeriya ta dauki matakan hana Coronavirus shiga kasar

An wallafa

Latsa alamar lasifika don sauraren hira da Dakta Abubakar Jafiya

Hukumomi a Najeriya sun ce sun fara daukar matakan ko-ta-kwana kan cutar Coronavirus.

Dakta Abubakar Jafiya na cibiyar yaki da cututtuka a Najeriya ya shaida wa BBC cewa a shirye Najeriya take domin hana cutar shigowa kasar.

Ya kuma ce gwajin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi na matakin da Najeriya ta ke na hadarin kamuwa da cutar ba shi da yawa, don haka yiwuwar kamuwa da cutar a Najeriya ba shi da yawa.

"Baya ga wannan mun hada kai da abokan huldarmu na kiwon lafiya mun shirya wasu mutane na musamman da ke shirin ko ta kwana dangane da cutar ko da za ta shigo mana," a cewarsa.

Ya ce suna duba abubuwan da za a gyara a fannin asibitoci da kayan aiki.

Haka kuma, Dakta Abubakar ya ce akwai ma'aikata a duka hanyoyin shigowa Najeriya da aka ajiye don tantance masu shigowa kasar daga kasashen waje.

Ya ce "Yawanci mun fi mayar da hankali kan baki da ke shigowa daga China tunda a sauran kasashen an gano cewa mafi yawan wadanda suka shiga da cutar daga China suka fito."

Ya ce akwai asibitoci na musamman da aka zaba a wasu jihohin Najeriya don ajiye wadanda ake tunanin sun kamu da cutar Coronavirus, kuma jihohi ne da ke da filin jirgin sama kamar Legas da Abuja da Kano.

An yi haka ne saboda baki masu shigowa ta jirgin sama.

Dakta Abubakar ya ce kawo yanzu ba a samu wani da ya nuna alamun cutar ba a Najeriya.

Cutar Coronavirus dai ta samo asali ne daga birnin Wuhan na China, kuma cuta ce da ke shafar numfashi kuma ta ke da saurin kisa.

Kawo yanzu ta kashe sama da mutam dari da hamsin a China kuma tana kara yaduwa zuwa sauran kasashen duniya kamar Amurka da Faransa da Thailand da Japan da sauransu.