Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Daliban Ghana sun kosa su bar China saboda Coronavirus
Wani dalibi dan kasar Ghana ya bayyana wa BBC halin dimuwa da daliban wasu kasashe ke ciki a birnin Wuhan na kasar China, wanda ke rufe biyo bayan barkewar cutar coronavirus mai saurin kisa.
A ranar Litinin ne, babban jami'in gwamnatin China Li Keqiang ya ziyarci Wuhan, babban birnin lardin Hubei, inda aka samu barkewar cutar.
Adadin mutanen da cutar ta halaka a China ya karu zuwa 81, sannan kusan mutum 3,000 ne aka tabbatar ba su da lafiya.
A hirarsa da BBC, dalibin wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce: ''Muna cikin fargaba saboda adadin kullum karuwa yake.
"A dakunan kwananmu, idan ka hadu da mutum, sai ya matsa can gefe. Babu mai son ya kusanci wani.
''Mata na kuka, suna so su koma gida. Suna cikin fargaba. Ba su da sauran tabbas. Ba ma so mu zauna a nan''.