Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana gudanar da zaben cike gurbi a wasu jihohin Najeriya
A ranar Asabar 25 ga watan Janairun 2020 ne dai Hukumar Zaben Najeriya INEC ke gudanar da zaben cike gurbi a wasu daga cikin jihohin kasar.
Ana gudanar da zabukan ne a jihohi 11 inda cike gurbin ya shafi kananan hukumomi 33 a wadannan jihohi.
Jihohin da ake yin zaben cike gurbin sun hada da Abia da Akwa-Ibom da Bauchi da Benue da Cross River da Imo da Kano da Kaduna da Niger da Ogun da Sokoto.
Kamar yadda Hukumar INEC din ta bayyana, zaben ya kunshi cike gurbin dan majalisar dattawa daya da 'yan majalisun wakilan tarayya 12 sai kuma na majalisar jihohi 15.
Tuni dai hukumar zaben ta fara wallafa hotuna a shafinta na Twitter kan yadda aka fara gudanar da wadannan zabuka na cike gurbi a wasu mazabun.
Tun a baya dai, hukumar INEC din ta bayyana cewa kara 807 aka shigar bayan babban zaben, inda kotu ta kori kara 582 daga ciki, inda 183 kuma masu karar ne suka janye da kansu, 12 kuma kotu ce ta tabbatar da zaben su, sa'annan ta bukaci a sake gudanar da zabe a mazabu 30.
Tuni dai aka yi biyu daga cikin 30 din a watan Nuwambar bara a mazabar dan majalisar tarayya ta Ajaokuta, da ta dan majalisar dattawa ta Kogi ta yamma.