Kotun Koli ta tabbatar wa Tambuwal kujerar gwamnan Sokoto

An wallafa

A ranar Litinin ne Kotun Koli ta yi watsi da karar da Ahmed Aliyu na APC a jihar Sokoto ya shigar gabanta, inda kotun ta tabbatar da Aminu Waziri Tambuwal na PDP a matsayin gwamnan jihar.

Wannan hukunci na nufin Ahmad Aliyu na APC ba zai iya sake kai kara ko ina ba, sai dai ya hakura.

Tun a ranar 2 ga watan Oktoban bara kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar ta yanke hukunci kan zaben inda ta yi watsi da koken da dan takarar jam'iyyar APC ya shigar a gabanta inda yake kalubalantar nasarar da gwamnan jihar yayi kuma dan jam'iyyar PDP wato Aminu Waziri Tambuwal.

Tambuwal ya yi nasara a zaben Sokoton da kuri'u 512,002, bayan da ya doke abokin hamayyarsa, Ahmed Aliyu da ya samu kuri'u 511,660.

Bayan haka dan takarar APC din ya daukaka kara zuwa kotun sauraron kararrakin zabe inda a nan ma kotun ta yi watsi da karar da ya kai inda ta jaddada hukunci da kotun sauraren kararrakin zabe ta yi a baya.

A wannan dalili ne ya sa Ahmed ya kara daukaka kara zuwa Kotun Koli domin kalubalantar Tambuwal.