Mutum 12 sun mutu a hadarin mota a Kano

An wallafa

Akalla mutum 12 ne suka mutu a wani hadarin motoci da ya afku a kauyen Tsaida da ke karamar hukumar Gaya a jahar Kano.

A cewar hukumar kiyaye hadura Najeriya, FRSC, hadarin dai ya rutsa da maza takwas da yara uku da mace daya.

FRSC ta kara da cewa sauran fasinjoji 26 da suka samu jikkata suna karbar magani a babban asibitin karamar hukumar ta Gaya.

Hukumar ta ce da misalin karfe 11 na safe ne wata motar fasinja mai cin mutum 18 kirar Hummer da mai cin mutum takwas kirar Hiace ne suka yi taho mu-gama sakamakon gudun wuce sa'a.

FRSC ta kuma ce tana ci gaba da aikin tantance shaidar tuki bisa la'akari da yadda wasu direbobi ke tukun ganganci a titunan Najeriya.

Ana dai dora alhakin yawan hadurran ababan hawa ga gangancin masu tuki da rashin iya tukin da kuma rashin kyawun hanyoyi a fadin kasar.