Yadda injiniyan sinadarai ya zama mai wankin takalmi

    • Marubuci, Wegene Alemayehu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Amharic
  • An wallafa

Chekole Menberu, da yanzu yake cika shekara 27 ya kasance mai buri a lokacin da ya kammala karatun injiniya a bangaren sinadarai shekara biyu da suka gabata a Ethiopia.

Lamari ne na dadadawa la'akari da irin kalubalen da ya fuskanta kafin kaiwa ga wannan mataki.

Tsawon shekaru, Chekole ya kasance mai bi layi-layi yana gyaran takalma domin biyan bukatunsa.

Tun daga tasowarsa Mr Chekole ya yi ta fafutukar samun abin yi.

Mahaifinsa ya mutu a lokacin da yake yaro kuma ya koma zama da kakanninsa a Fogera a yankin Amhara. Mahifiyarsa kuma ta yi wani auren.

'Na yi ta nacin zuwa makaranta'

Mr Chekole dai yana da sha'awar zuwa makaranta sai dai kakanninsa ba su iya biyan kudin makarantarsa ba da sauran bukatunsa.

Haka ce ta sa ya koma zama tare da kawunsa, inda yake kiwon dabbobi. Amma ya ci gaba da fatan kakanninsa za su tallafa masa.

Ya fada wa BBC cewa "na ci gaba da damun kakannina su tura ni makaranta."

Daga bisani, kakansa ya amince da bukatarsa, inda ya sanya shi a wata makaranta a Woreta.

Sai dai taimakon kakan nasa ya kasance na wani dan lokaci a lokacin da yake aji na biyu.

''Dole ta sa na tashi haikan domin taimaka wa kaina'' a cewar Mr Chekole.

"Da taimakon wani abokina wanda yake wankin takalmi, na fara wankin takalmi ni ma."

Daga aji na uku har zuwa lokacin da ya shiga jami'a, Mr Chekole ne ya dauki nauyin kansa ta hanyar yin amfani da kudin da yake samu daga wankin takalmi bayan ya tashi daga makaranta.

"Na dauka sana'ar wankin takalmi za ta taimaka min. A lokacin nakan shafe rabin rana ina aiki sauran lokacin kuma ina amfani da shi wajen yin karatu" a cewarsa.

"Al'amura ba su zo ta sauki ba amma na kan samu kwarin gwiwa idan na ji labarin wasu da suma suka shiga halin da na shiga har suka zama liktoci da injiniyoyi."

'Na shiga damuwa'

Yana shiga wani hali a duk lokacin da sabuwar shekarar karatu ta kama saboda sayen kayan makaranta wanda ba shi da halin saye.

"Na sha wahala kan karatu," kamar yadda Mr Chekole ya fada.

"Na fuskanci kalubale da dama amma ba zan manta irin wahalar da na sha ba a shekarun da na shiga aji na takwas da 10 da kuma shekarar da na shiga jami'a."

Duk da irin matsalolin da ya fuskanta, a 2013 ya yi kokarin shiga jami'ar Bahir Dar da ke babban birnin Ethiopia, inda ya yi karatun injiniya a bangaren sinadarai.

"Akwai jita-jitar da ake yadawa cewa kasar Ethiopia tana bukatar injiniyoyi a masana'antu kuma abin da ya sa kenan na yanke shawarar yin karatun injiniya saboda ina fatan na samu aiki da zarar na kammala karatuna," a cewarsa.

Bai sha irin wahalar da ya sha a baya ba a shekara biyar din da ya yi a jami'a. Wata takarda da aka aike daga garinsu zuwa jami'ar da yake karatu cewa ba shi da wanda yake tallafa masa, ya sa jami'ar take biyansa birr 200, kimanin dala 10 duk wata.

"Ina kuma samun tallafi daga abokaina da wadanda muke kwana tare da su sai dai da ranar da zan kammala jami'a ta tunkaro na kasance cikin farin ciki, ina tunanin abin da zan yi bayan gama makaranta.

"Na shiga damuwa idan na yi tunanin zan kasance ba ni da aiki," in ji Mr Chekole.

'Ba ni da rabo'

A 2017, Mr Chekole ya kammala digirinsa na farko a fannin injiniyan sinadarai kuma babban abin da ke gabansa shi ne samun aikin yi.

Sai dai bai samu nasara ba.

"Na shafe wata uku ina neman aiki a babban birnin Ethiopia, Adis Ababa. Na yi zagaye daga wannan masana'anta zuwa waccan cikin birnin domin neman aikin yi amma hakan ba ta samu ba."

Ya ziyarci yankunan kasar har ma ya je Woldia mai nisan kilomita 250, arewa da Adis Ababa don neman aikin yi.

"Na nemi aiki a wuraren da ba wanda ya yi karatun jami'a suke nema ba amma ban samu aiki ba saboda masu wajen na tunanin idan suka ba ni aikin a gaba zan nemi a kara min matsayi."

Ya fara aiki a wata masana'anta inda ake biyansa birr 29 kimanin dala guda kowace rana, amma bai dade da fara aikin ba ya bari saboda abin da ake biyansa ba zai ishe shi tafiyar da harkokinsa na yau da kullum ba.

Duk da irin ci gaban da tattalin arzikin Ethiopia ya samu, kashi biyu bisa uku na matasan kasar (masu shekara tsakanin 15 zuwa 29) da ke zaune a birane basu da aikin yi a 2018 kuma adadin ya karu ne daga kashi 22 cikin dari da ake da shi a 2016, a cewar hukumar kididdiga ta kasar.

Wannan ne ya sa Mr Chekole shi ma ya bi sahun masu digirin da ba su da aikin yi neman taimako daga gwamnati amma kuma gwamnatin ta ce ba ta da kudin biyan daliban da suka kammala karatun injiniya a bangaren sinadarai.

Jami'a

Bayan shafe watanni yana neman aiki ba tare da ya samu ba, Chekole ya koma Bahir Dar - don yin aikin da bai taba tunanin zai koma gare shi ba.

"Lokacin da ya zama ba ni da wani zabi, kawai na yanke shawarar komawa sana'ar wankin takalmi."

Dangane da ko yana da na sanin zuwa makaranta, ya ce da ace bai yi makaranta ba, da fushin da yake yi ba zai kai haka ba.

"Karatun da na yi ya sa ni cikin wani yanayi sannan babu wani tagomashi da na samu bayan na kammala shi," inda ya ce "da bai sadaukar da abubuwa da dama ba domin karatun."

Mr Chekole ya koka kan ydda gwamnatin Ehiopia ta fi mayar da hankali kan siyasa da batun tsaro a maimakon samar da ayyukan yi ga marasa aiki.

"Malamai na da suka sanni tun ina jami'a un yi matukar kaduwa amma wasu na bani kwarin gwiwa a lokutan kuma har su bani kudi."

"Abokai na kuma suna yawan zuwa na wanke musu takalma ko da kuwa takalman a goge suke domin dai kawai su bani kudi."

Mr Chekole ya ce har yanzu bai fidda ran samun aikin yi ba duk da kalubalen da ya fuskanta.

A cewarsa, "har yanzu ina zuwa ina duba wuraren tallata guraben ayyukan yi ko zan da ce da samun aikin yi."