Ina neman rigar kariya daga majalisa - Netanyahu

An wallafa

Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yanke shawarar neman rigar kariya daga majalisa domin ka da a hukunta shi kan tuhume-tuhumen da ake yi masa na rashawa da cin hanci.

Matakin dai ana ganin zai haddasa tsaikon gurfanar da Netanyahu a gaban kotu har zuwa lokacin da za a gudanar da sabbin zabe a watan Maris.

A watan Nuwamba, an tuhumi firai minista Netanyahu da rashawa da zamba cikin aminci da saba ka'idar aikinsa na firai minista a cikin wasu batutuwa guda uku.

Mr Netanyahu ya musanta aikata laifuka da ake tuhumar sa da su na bukatar hadin kan 'yan majalisar dokoki fiye da rabi kafin ya samu rigar kariyar.

Ana zargin Mr Netanyahu dai wanda shi ne firai ministan da ya fi kowanne dadewa a kasar, da karbar kyautuka daga masu wadata.

Netanyahu ya nemi rigar kariyar ne ta hanyar wani jawabi da ya yi a gidan talbijin din kasar, sa'o'i hudu kafin wa'adin neman kariyar ya zo karshe.