Saudi Arabia: An haramta auren 'yan kasa da shekara 18

An wallafa

Ma'aikatar Harkokin Shari'a ta kasar Saudiyya ta haramta aure tsakanin 'yan kasa da shekara 18 sannan ta saka 18 din a matsayin mafi karancin shekarun aure a kasar.

Ministan Shari'a Sheikh Dr. Walid Al-Samaani ne ya bayar da umarnin ga kotuna, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito a ranar Litinin.

Batutuwa irin wadannan za a mika su ne ga kotu ta musamman domin duba su karkashin dokar kare hakkin yara.

Umarnin da ministan ya bayar yana karkashin sakin layi na 16/3 na dokar ta kare hakkin yara wanda ya ce:

"Kafin a kulla yarjejeniyar aure wajibi mutum ya tabbatar cewa auren 'yan kasa da shekara 18 ba zai zama matsala a gare su ba sannan kuma da izininsu aka daura shi, mace ko namiji."

Kasar Saudiyya tana gudanar da sauye-sauye a yunkurinta na sajewa da sauran manyan kasashen duniya da kuma guje wa suka da take sha game da zargin take hakkin dan Adam.