Kotun koli ta tabbatar da nasarar el-Rufai da Masari da A A Sule

An wallafa

A Najeriya kotun koli ta tabbatar da zabukan wasu gwamnaonin kasar na zaben da aka yi a watan Maris din 2019.

A ranar Laraba ne tawagar alkalai bakwai na kotun karkashin jagorancin Mai Shari'a Mary Odili ta tabbatar da nasarar Nasir El-Rufai a matsayin gwamnan jihar Kaduna da Abdullahi Sule a matsayin zababben gwamnan jihar Nassarawa.

Mai Shari'a Mary Peter-Odili ta ya watsi da daukaka karar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP ya yi na kalubalantar zaben Gwamna Sule.

Alkalan sun ce mai daukaka karar da jam'iyyarsa ta PDP ba su da kwararan hujjoji.

Kazalika kotun ta tabbatra da nasarar gwamnan jihar katsina Aminu Bello Masari da na jihar Legas Babajide Sanwo-Olu bayan ta yi watsi da kararrakin da aka shigar masu kalubalantar zabensa.

Kotun ta kuma tabbatar da nasarar Seyi Makinde a zaben gwamnan jihar Oyo.

Kotun kolin ya yi watsi da hukuncin kotun daukaka karar da ta soke hukuncin da kotun sauraren karar zaben gwamnan jihar wadda ta yi watsi da karar da jam'iyyar APC da dan takararta Adebayo Adelabu.

APC da Adelabu na kalubalantar nasarar Makinde a zaben.

Kotun daukaka karar ta ce kotun sauraren kararrakin zaben ta yi kuskure wajen yin watsi da korafin jam'iyyar APC, amma ta ki tsige Makinde a matsayin gwamnan Oyo.

Amma kotun koli ta soke hukuncin a ranar Laraba.