Zaben Burtaniya: 'Ba zan jagoranci 'yan Labour ba a zabe na gaba'

Asalin hoton, Reuters
Jeremy Corbyn ya ce ba zai jagoranci jam'iyyar Labour ba a zabe na gaba, bayan da jam'iyyar ta fadi warwas.
Ya ce zai ci gaba da zama shugaban jam'iyyar a lokacin da zai yi zurfin tunani kan sakamakon zaben, wanda shi ne mafi muni ga jam'iyyar tun 1935.
Ya kara da cewa batun ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai ya rarraba kai a siyasa.
Amma wasu 'yan jam'iyyar, ciki har da 'yan majalisar da suka rasa kujerunsu, sun zargin jagorancin Mista Corbyn da taka rawa wajen faduwa zaben.
Jam'iyyar ta rasa jerin yankuna masu karfi a arewacin Ingila da Wales, a wuraren da suka zabi ficewa daga EU lokacin da aka yi zaben raba gardama.
Jam'iyyar Conservatives ta yi gagarumar nasara a gaba daya kasar.
A lokacin da yake magana bayan ya yi nasarar cin zaben kujerarsa ta North Islington, Mista Corbyn ya ce manufofin jam'iyyar sun samu karbuwa sosai, kuma ya soki yadda kafofin yada labarai suka taso jam'iyyarsa a gaba.
Amma ya kara da cewa: "Batun ficewar kasar ya rarraba kasarnan, ya mamaye duk wata muhawara da aka saba kan siyasa."
"Na gane cewa wannan ya taimakawa wajen irin sakamakon da jam'iyyar Labour ta samu a fadin kasar na."
Labour dai ta shiga zaben ne da alkawarin sake tattauna yarjejeniyar Firayim Minista Boris Johnson ta Brexit, sannan a sake yin zaben raba gardama tare da zabin cewa Burtaniya za ta iya ci gaba da zama aEU.
Wannan shirin ya sha suka daga shugaban jam'iyyar Ian Lavery, wanda ya ce tsarin ya sa masu kada kuri'a masu goyon bayan jam'iyyar Labour ganin kamar jam'iyyar na goyon bayan zaman Burtaniya a EU ne.
"Suna ganin cewa ya kamata a ce an saurare su - kuma suna ganin cewa jam'iyyar Labour ta yi amai ta lashe kan sakamakon," a cewarsa.
Amma ya ce shirin ba na Jeremy Corbyn ba ne, tunda wakilan jam'iyya sun amince da shi da aka yi taro a watan satumba.










