Hannayen jarin Aramco su ne mafi daraja a duniya

An wallafa

Hannayen jarin kamfanin man Saudiyya na Aramco sun yi tashin gwauron zabi inda yanzu su ne mafiya daraja a duniya.

Hannayen jarin Aramco sun samu karin tagomashi da kashi goma a kan farashin da aka fara sanarwa, a lokaicn kaddamar da su a birnin Riyadh.

A makon jiya ne kamfanin wanda ke samar da fiye da kashi 10 na danyen mai a kasuwannin duniya ya samu dala biliyan 25.6 (fam biliyan 19.5).

Saudiyya ta fara sayar da hannayen jari a kamfanonin gwamnatin kasar ne a yunkurin masarautar na rage dogaron kasar a kan albarkatun mai.

Kasar za ta yi amfani da kudaden da ta samu daga sayar da hannayen jarin a bangarorin da ba na makamashi ba.

Karuwar farashin hannayen jarin Aramco da kashi 10 a yau ya sa darajarsu kaiwa kimanin dala tiriliyan 1.88, a cewar kasuwar hada-hadar hannun jarin Tadawul na kasar.

Hakan ya sa Aramco zama kamfani mafi daraja a kasuwannin duniya. Amma bai kai abin da Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman ya yi buri na dala tiriliyar biyun ba.

Hannayen jarin da su ne mafi daraja a duniya, sun zarce na kamfanin Alibaba na kasar China da a 2014 ya kai dala biliyan 25 a kasuwar hada-hadar hannun jarin Amurka.

Ta yaya aka yi?

Hakan ta faru ne bayan gwajin da Saudiyya ta yi na sayar da hannayen jarin ga 'yan kasuwa.

Kasar ta fi karkata ga masu zuba jari na cikin gida da na yankin Gabas ta tsakiya wajen sayar da kashi 1.5 na hannayen jarin.

Masarautar ta yi hakan ne bayan ta ga masu zuba jari daga kasashen ketare na yin dari-dari wajen karbar tayin da ta yi musu.

Da farko kasar ta yi nufin samun dala biliyan 100 a kasuwannin hannayen jari guda biyu - Tadawul na cikin kasar da kuma wani daga cikin kasuwannin kasashen ketare.

Amma kasar ta sauya dabarar ne bayan 'yan kasuwa daga kasashen waje sun nuna mata damuwarsu game da sauyin yanayi da barazanar siyasa da kuma rashin gudanar da harkokin kamfanoni a fili.

Kamfanononin kasashen duniyar ba su gamsu da darajar kadarorin kamfani ba, abin da ya sa Aramco janye taron zawarcin 'yan kasuwa da ta shirya gudanarwa a biranen New York da London.

Maimakon haka, sai ta mayar da hankalinta kan 'yan kasuwa na cikin gida da attajirai daga yankin Gulf. Bankunan kasar kuma sun yi ta ba wa 'yan kasar rance domin sayen hannun jarin Aramco, bayan wani gangami da aka yi a fadin kasar.

Sayar da hannayen jarin kamfanin na daga cikin manyan matakan da kasar ta dauka na zamanantar da tattalin arzikinta da kuma kawo karshen dogaronta a kan mai.

Yanzu kasar na bukatar gomman biliyoyin daloli cikin gaggawa domin aiwatar da wasu manyan ayyuka da gina sabbin masana'antu.

Sharhi: Sameer Hashimi, Wakilin BBC na kasuwanci a Gabas ta tsakiya

Ana kyautata zaton hannayen jarin Aramco za su yi tagomashi sosai tun da farko, ganin yadda tsarin ya samu karbuwa a wajen attajirai da kamfanonin kasar da aka bukaci su zuba jari a kamfanin.

Su ma kasashen yankin Gulf masu dasawa da Saudiyya irinsu Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait sun taimaka wurin kara darajar hannayen jarin Aramco ta hanyar sanya biliyoyin daloli a kamfanin.

Ma'aikatar makamashin Saudiyya na da kwarin gwiwar cewa darajar hannayen jarin Aramco za su kai dala tiriliyan biyu nan ba da jumawa ba.

Masu sharhi na hasashen cewa nan gaba hannayen jarin kamfanin za su cigaba da zama da wannan darajar. Amma sun ce dadewar hakan zai dogara ne ga yadda aka dore da daukar irin wadannan matakai.

Fara sayar da hannayen jari ga 'yan kasuwa na daga cikin manyan matakan da Saudiyya ke dauka domin karkatar da tattalin arzikinta daga dogaro a kan mai.

Yarima Mohammed bin Salman, wanda ke jagorantar shirin, na son yin amfani da wani yanki na kudaden da aka samu domin aiwatar da wasu tsare-tsare karkashin shirinta na 'Vision 2030'.

A karkashin shirin Saudiyya na neman zamanantar da tattalin arzikinta ta hanyar zuba jari da bude sabbin masana'antu da wasu manyan ayyuka na biliyoyin dala.