'Za a biya diyya kan wadanda suka rasu a Hajji'

An wallafa

Shugaban hukumar alhazan Najeriya mai barin gado, Barista Abdullahi Mukhtar ya ce kasar Saudiyya ta aike wa Najeriya kudaden diyya ga wadanda suka rasu ko kuma jikkata a aikin hajjin 2015.

A shekarar 2015 ne dai aka samu rikitowar na'urar gini kan alhazai, inda da dama daga cikin alhazai suka rasu ciki har da 'yan Najeriya.

Barista Abdullahi Mukhtar ya kuma bayyana shekarar ta 2015 da wadda ta fi tsaya masa a rai sakamakon rasuwar 'yan Najeriyar.

Dangane kuma da nada sabon shugaban hukumar ta alhazai da shugaba Buhari ya yi a makon jiya, Abdullahi Mukhtar ya ce mutumin da aka nada ya cancanta.

Latsa wannan alamar lasifika da ke kasa domin sauraron hirar Barista Abdullahi Mukhtar da Yusuf Yakasai.