Yadda yaro ya kafa shaida da abokan karatunsa

Asalin hoton, Kent County Court
Wani yaro dan shekara biyar a Michigan ya gayyaci abokan karatunsa da suke aji daya domin su shaida yadda wasu ma'aurata zasu karbi ragamar kula da shi, matakin da ya dadadawa al'umma rai a fadin duniya.
Yaron, mai suna Micheal a hukumance ya koma hannun sabbin iyayensa a kotun Kent County.
Wani hoto da aka wallafa a shafin Facebook ya nuna karamin yaron zaune kan kujera a harabar kotun, kusa da ma'auratan da yanzu za su rika kula da shi.
A bayan shi kuma, dalibai ne 'yan ajinsa cike da murna kuma suna rike da wani tsinke mai dauke da alamar 'so'.
Yayin da ake sauraron shari'ar, dukkanin daliban sun gabatar da kansu tare da yin bayanin dalilin da ya sa suka halarci kotun domin taya abokin karatunsu murna.
"Micheal babban aboki na ne'' a cewar wani yaro mai suna Steven.
Ita kuwa wata yarinya ta fada wa mai shari'a Patricia Gardner cewa sunanta Lily kuma tana kaunar Micheal''.
Malamar Micheal ta bayyana cewa ''sun fara zangon karatun kamar 'yan uwa inda ta ce zama 'yan uwa ba wai yana nufin sai ana da alaka ta jini ba saboda zama 'yan uwa na nufin kauna da taimaka wa juna''.

Asalin hoton, Kenty County Court
Daliban da malamai da kuma iyaye sun kasance masu sowa da tafi yayin da Micheal da iyayen da za su rika kula da shi suka buga katakon da alkalai ke rike wa, alamar cewa an kammala batun mika yaron hannunsu.
Ranar Alhamis ta yi daidai da zagayowar ranar mika yara ga sabbin iyalansu a kotun Kent County inda kuma aka mika yara 37 ga iyalan da za su karbi ragamar kula da su, kamar yadda karamar hukumar ta Kent ta wallafa a shafinta na Facebook.
Mai shari'a Patricia ta kara da cewa gaba daya 'yan ajin Micheal sun zo shaida wannan abin tarihi a rayuwarsa su kuma nuna masa kauna da goyon baya''.
Micheal, a wani hoton bidiyo da aka nada a wajen harabar kotun ya ce ''ina kaunar mahaifina'', furucin da ya sa idon baban ya cika da kwalla.
Mutane sama da 100, 000 ne suka wallafa hoton a Facebook na Micheal da 'yan ajinsa.










