Pisa tests: Wacce kasa ce ta fi dalibai masu hazaka?

Asalin hoton, Getty Images
Wacce kasa ce ta fi ingantaccen tsarin ilimi?
Bayar da amsar wannan tambaya ba zai yi wuya ba, to amma wani shiri na duba kwazon dalibai daga sassa daban-daban na duniya ya saukaka komai ta hanyar bayyana mana amsa.
Wani shiri ne da kungiyar da ke sa ido kan tattalin arziki da ci gaba OECD take jagoranta, kuma sun fara shirin ne tun shekarar 2000 suka fara bincike kan dalibai 'yan shekara 15 a kowacce shekara uku.
Kungiyar OECD ta fitar da sakamako na baya-bayan nan a ranar Talata, kan jarabawar da aka yi a shekarar 2018 da kuma ya nuna dalibai 'yan kasar China sun yi zarra kan dukkan kasashen duniya da aka yi nazari akai ta fannin son karatu, da ilimin lissafi da kimiyya.
Kasashen da aka yi nazari
Kasashe 79 ne suka shiga nazarin shekarar da ta gabata, kuma an yi ne a kan dalibai 600,000.
Daman dai kasashe 37 da suka ci gaba a duniya ne suka samar da hukumar Pisa wadanda suka hada da Amurka, da Japan da mambobin kungiyar Tarayyar Turai.
Sai dai wasu karin kasashen sun shiga don gwamnatoci na son sanin matsayin dalibansu idan aka kwatanta da na sauran kasashe.
Ana yi wa daliban jarabawa mai tsauri, inda ake gabatar musu wani kalubale na rayuwa, wanda ya hada da yanke shawara kan yadda za su kashe kudi da amfani da bayanai.
Misali a shekarar 2018 an sanya tambaya akan wani mai kiwon kaji ne ya ke son sanin ko babu abin da zai faru idan ya bai wa kazarsa maganin asfirin, wannan tambaya ce mai tsauri.
Daliban Asiya sun mamaye wajen
Daliban China su ne a sahun gaba har sau uku cikin gwaji hudu da Oisa ta yi, sai dai kuma an tsaurara wajen zabo daliban daga wasu yankunan kasar.
Hukumomin China sun fi amfani da sakamakon da aka samu daga daliban yankin Shangai a shekarar 2009, a 2015 da 2018 an bayyana sakamakon gudumomi hudu ne na kasar.
A wata sanarwa da daraktan ilimi na OECD Andreas Schleicher ya fitar, ya ce "A wadannan fannonin daliban da ba sa samun gata sun fi mayar da hankali a fannin karatu, idan aka kwatanta da sauran.''
Kasar Finland ta samu shiga nazarin Pisa har sau uku, a shekarun 2000 da 2003 da kuma 2006, yayin da Singapore ta shiga sau daya a shekarar 2015.

Asalin hoton, Getty Images
Ta bayyana karara kasashen yankin Asiya ne suka fi sauran kasashe rawar gani a nazarin, sakamako na baya-bayan nan ya nuna kasashen yankin sun lashe matsayi na daya zuwa na hudu a teburi, sannan kasar Estonia ce kadai da ta yi nasara wadda ba a yankin Asiya take ba.
Wata damuwa da aka nuna kan sakamakon, ya nuna akwai tazara mai yawan gaske tsakanin daliban kasashen da suka ci gaba da masu tasowa.
Wani abu da OECD ta gano ya nuna akwai banbanci sosai tsakanin maza da mata da akai nazarin kwazonsu.
Misali mata sun doke maza ta fannin son karatu, sannan akwai 'yar rata tsakaninsu ta fannin kimiyya da kusan maki biyu. Yayin da maza suka yi musu zarra da maki biyar ta fannin lissafi.










