Burkina Faso: An kashe mutum 14 a harin coci

Map of Burkina Faso
An wallafa

A kalal mutum 14 ne suka rasa rayukansu bayan da wasu 'yan bindiga suka bude wuta a cikin wani coci da ke Burkina Faso

Mamatan na halartar ayyukan ibada a ranar Lahadi ne a wata majami'a da ke Hantoukoura, wanda ke gabashin kasar.

Ba a san ko suwa ne ne suka kai wannan harin ba, kuma babu wani bayani kan dalilansu na yin wannan aika-aika.

Wata sanarwa da gwamnatin yankin ta fitar na cewa mutane da dama sun sami raunuka.

Wata majiyar jami'an tsaro ya sanr da kamfanin dillancin labarai na AFP cewa wasu 'yan bindiga ne suka kai harin, inda ya ce sun "harbe mabiya addinin Kirista har da faston cocin da wasu kananan yara,"

A watan Oktoba an kashe mutum 15 a wani hari da aka kai kan wani masallaci a kasar.

Hare-hare masu alaka da addini sai karuwa suke yi a Burkina Faso tun 2015, wanda ya tilastawa hukumomi rufe dubban makarantun kasar.