Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari zai dora tubalin ginin jami'ar sufuri a Daura
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai dora tubalin ginin jam'iar sufuri wadda irin ta ce ta farko a kasar.
Ana sa ran a mako mai zuwa ne shugaban zai dora tubalin ginin a mahaifarsa da ke Daura a jihar Katsina.
Kamar yadda hukumar da ke kula da jami'oi ta Najeriya ta bayyana a shafinta na intanet, ana sa ran cewa aikin zai lashe kusan naira biliyan 18.
A wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Abuja, Ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi ya bayyana cewa tuni aka bai wa kamfanin gine-gine na China Civil and Construction Company wato CCECC, kwangilar gina jami'ar kuma aikin zai kankama da zaran gwamnan jihar Katsina ya bayar da filin da za a gudanar da aikin.
Ministan ya bayyana cewa akwai matasa 'yan Najeriya da suka samu tallafi daga gwamnatin Najeriya domin karatu a kasar China inda suke karanta fannin aikin injiniya na jirgin kasa da layin dogo.
Ya ce da zaran sun kammala karatun, za a tura su wannan sabuwar jami'ar da za a gina ta daura su fara koyarwa kafin su kama aiki gadan-gadan.