Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 ga shugaban kasar Suriname

An wallafa

An yanke wa Shugaban kasar Suriname Desi Bouterse daurin shekaru 20 a gidan yari sakamakon samunsa da laifin kisan abokan adawa 15 tun a 1982.

Bouterse mai shekaru 74, wanda a yanzu haka ya kai ziyarar aiki China na da makonni biyu ne kacal ya daukaka kara kan wannan hukunci da kotun ta yanke.

Kotun ta ce ta same shi da laifin shiryawa da kuma bayar da umarnin kashe fursunonin siyasa 15 ba bisa ka'ida ba ko kuma ba ta hanyar shari'a ba.

Tun a baya dai Shugaba Bouterse ya musanta wannan zargin da ake yi masa.

Sai dai ya hakikance a kan cewa wadanda aka kashe, cikinsu harda wasu lauyoyi da kuma shugabannin kungiyoyi da kuma 'yan jarida, an harbe su ne a yayin da suke kokarin tsallake wata katanaga tun ta mulkin mallaka a Paramaribo babban birnin kasar.

Shugaba Bouterse ya jagoranci Suriname tun a shekarun 1980 a matsayin Shugaban kasar na mulkin soja.

Ya zama shugaban kasar na mulkin dimokradiyya a 2010 bayan zabe da aka gudanar, haka zalika an kara zabarsa a matsayin shugaban kasar a wa'adi na biyu a 2015.

Kotun ta ce shugaban ya sa ido kan wani farmaki inda sojojin da ke karkashin kulawarsa suka yi garkuwa da masu caccakar gwamnati 16 ciki harda lauyoyi da 'yan jaridu da kuma malaman jami'a.

Mutum daya cikin 16 ne kawai ya tsira wanda shugaban wata kungiya ne kuma ya bayar da shaida a gaban kotu kan Shugaba Bouterse.