Hotunan zanga-zanga kan dokar kalaman kiyayya a Najeriya

An wallafa

Wasu 'yan Najeriya suna zanga-zangar nuna kin amincewarsu game da kudirin dokar nan ta kalaman kiyayya wato Hate Speech Bill, wanda Sanata Alyu Abdullahi Sabi ya gabatar a Majalisar Dattawa.

zanga-zangar adawa da kalaman kiyayya
Bayanan hoto, Wasu 'yan Najeriya suna zanga-zangar nuna kin amincewarsu game da kudirin dokar nan ta kalaman kiyayya wato Hate Speech Bill, wanda Sanata Aliyu Abdullahi Sabi ya gabatar a Majalisar Dattawa.
zanga-zangar adawa da kalaman kiyayya
Bayanan hoto, Ana zanga-zangar ne a Legas da Abuja.
zanga-zangar adawa da kalaman kiyayya
Bayanan hoto, Tun sanda sanatan ya gabatar da kudirin dokar 'yan Najeriya suka yi Allah-wadai da shi musamman ayar da ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya furta kalaman kiyayya kuma ya yi sanadin ran wani to shi ma za a dauki ransa ta hanyar rataya.
zanga-zangar adawa da kalaman kiyayya
Bayanan hoto, Zanga-zangar tana gudana ne a farfajiyar zauren majalisar a safiyar ranar Laraba tare da yin kira ga shugabannin majalisun tarayya da su dakile shirinsu na yin dokar.
zanga-zangar adawa da kalaman kiyayya
Bayanan hoto, Tun 12 ga watan Nuwamba ne dokar ta tsallake karatu na farko a zauren majalisar.
zanga-zangar adawa da kalaman kiyayya
Bayanan hoto, A yanzu dokar tana jiran karatu na biyu.
zanga-zangar adawa da kalaman kiyayya
Bayanan hoto, Sai dai a wani bayani da ya fitar ranar Lahadi, Sanata Aliyu Abdullahi ya ce "kudurin zai fuskanci 'yan gyararraki musamman ayar da ta tanadi hukuncin kisa wanda 'yan Najeriya suka fi kokawa a kansa" idan sun tashi sake muhawara a kan dokar.
zanga-zangar adawa da kalaman kiyayya
Bayanan hoto, Kazalika, Sanatan ya bayyana a wani bidiyo da shafin Majalisar Dattawa ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda yake cewa kudirin dokar ya tanadi cewa hukuma ce mai zaman kanta za a kafa da za ta kula da irin wadannan laifiuka.
zanga-zangar adawa da kalaman kiyayya
Bayanan hoto, Sanatan ya kara da cewa sai wannan hukuma ta duba ta tabbatar da cewa kalaman da mutum ya yi sun kai munzalin kalaman kiyayya (hate speech) sannan su bayar da shawarar dokar ta yi aiki a kansa.