British Airways ya gamu da matsala a hanyar zuwa Abuja

Jirgin British Airways

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jirgin ya taso ne daga filin jirgi na Heathrow da ke birnin Landan
An wallafa

Kamfanin jiragen sama na British Airways ya ce wani jirginsa ya samu 'yar karamar matsalar na'ura yayin da yake sararin samaniya a kan hanyarsa ta zuwa Abuja a Najeriya daga birnin Landan.

Hakan ya sa matukin jirgin ya juya akalarsa ya koma Landan, inda fasinjoji da ma'aikatan jirgin suka samu tarba daga jami'an bayar da kulawar gaggawa, wadanda suke cikin shirin ko-ta-kwana.

Kamfanin dai ya kai fasinjojin otal, inda suka kwana a can.

Sai dai har yanzu ba a san wace irin matsala jirgin ya samu ba.