Birtaniya ta kulla yarjejeniya da 'yan kasuwar Najeriya

UK-Africa Investment Summit

Asalin hoton, UK-Africa Investment Summit

An wallafa

Sashen kasuwanci na kasa da kasa na gwamnatin Birtaniya ya karbi bakuncin wasu 'yan kasuwa daga Najeriya kusan 100, inda suka fitar da sashen noma da makamashi da lafiya da ayyukan raya kasa da kuma fasahar sadarwa wato ICT a cikin yarjejeniyar.

Taron ya zo ne yayin da ake shirin gudanar da taron zuba jari tsakanin Birtaniya da kasashen Afirka na 2020 da za a yi ranar 20 ga Janairun 2020. Taron zai duba hanyoyin guduwa da kuma tsira tare da kuma kirkirar ayyukan yi.

Yayin da yake jawabin bude taron a ranar Laraba, magajin birnin Landan Sir Charles Bowman, ya bayyana cewa da ma can Birtaniya babbar kawar kasashen Afirka ce a fannin zuba jari.

"Najeriya ce kasa ta biyu da Birtaniya ta fi zuba jari, inda ta zuba fan biliyan biyar sannan kuma kamfanoni kusan 100 ne suke harkokinsu a kasar. Harkokin kasuwanci da aka yi tsakanin Najeriya da Birtaniya a shekarun 2018 zuwa 2019 ya kai fan biliyan biyar, wanda ya karu da kashi 9% a kan shekarun baya.

Shi kuwa ministan kasuwancoi da zuba jari na Najeriya Adeniyi Adebayo cewa ya yi:

"Tuni Najeriya ta fara aiwatar da wasu sababbin sauye-sauye domin saukaka harkokin kasuwanci sannan kuma tana agaza wa masu zuba jari da kuma yarjejeniya tsakaninta da wasu kasashe."

Mataimakin wakilin Birtaniya a Najeriya Harriet Thompson ne ya tsaya wa kamfanonin Najeriyar yayin da suke gabatar da hajojinsu ga masu zuba jariin a birnin Landan.

Birtaniya dai tana yunkurin zama kasa lamba daya mafi yawan zuba jari a nahiyar Afirka, a cikin kasashe bakwai mafiya karfin tattalin arziki a duniya wato G7.