Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya taya Atiku jimami kan rasuwar mai taimaka masa
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya taya babban abokin hamayyarsa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar jimami kan rasuwar wani mai taimaka masa Alhaji Umar Pariya.
Wata sanarwa da mai bai wa shugaban na Najeriya shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya fitar, Buhari ya ce rasuwar Alhaji Pariya ta girgiza shi.
Sannan ya yi masa addu'ar Allah ya yafe masa kurakuransa tare da bai wa Atiku hakurin rashinsa.
Haka ma mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya wallafa sakon ta'aziyar a Twitter.
Shugaba Buhari ya ce "na samu labarin rasuwar mataimakinka, Alhaji Pariya. Akwai kaduwa ganin yadda kuka dade tare da shi a matsayin mai taimaka maka. Ina addu'ar Allah ya jikanshi ya kuma bayar da hakurin rashinsa.''
Ya kara da nema wa mamacin gafarar Ubangiji.
Atiku Abubakar ya ce Umar Pariya matsayinsa ya wuce na mai taimakawa, ya kasance a matsayin dan uwa.