Diego Maradona: Gwarzon Argentina ya ajiye aikin horas da Gimnasia

Diego Maradona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Diego Maradona
An wallafa

Tsohon dan wasan Argentina Diego Maradona ya ajiye aikin horas da kungiyar kwallon kafa ta Gimnasia Esgrima La Plata, kasa da watanni uku kenan da ya karbi ragamar kungiyar.

Karo na farko kenan da tsohon dan wasan mai shekara 59 ya karbi aikin horas da 'yan wasa a kasarsa tun bayan shekarar 2010.

Maradona, wanda ya karbi ragamar jagorancin lokacin da kungiyar ke kasa a teburi, ya ci wasa uku daga cikin wasanni takwas kungiyar ta yi, inda ta koma mataki na 22 a kan teburi.

Gwarzon dan kwallon wanda ya lashe gasar cin kofin duniya a 1986 ya bar mukaminsa na baya a kungiyar Mexico rukuni na biyu sakamakon matsalar lafiyar da ya samu.

Aikin da Maradona ya yi a matsayin sa na mai horaswa

  • Textil Mandiyu (Oktobar 1994 zuwa Disambar 1994)
  • Racing Club (Janairun 1995 zuwa Maris din 1995)
  • Argentina (Oktobar 2008 zuwa Yulin 2010)
  • Al-Wasl (Mayun 2011 zuwa Yulin 2012)
  • Al-Fujairah SC (Mayun 2017 zuwa Afrilun 2018)
  • Dorados (Satumbar 2018 zuwa Yunin 2019)
  • Gimnasia (Satumbar 2019 zuwa Nuwambar 2019)