Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Na tsani allurar riga-kafi har sai da dana ya kamu da shan inna'
- Marubuci, Daga Charles Mgbolu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan harkar lafiya a Lagos
- An wallafa
Adamu Misa ya kasance daya daga cikin masu fatattakar jami'an lafiya da ke shiga gida-gida a arewacin Najeriya da nufin yi wa yara riga-kafi, amma tun bayan da dansa ya kamu da cutar shan inna sai ya daina.
Dansa mai suna Buhari mai shekara takwas, ya kwanta bacci lafiya kalau, amma da gari ya waye sai ya gagara tashi tsaye balle kuma ya yi tafiya.
Cikin kaduwa da tashin hankali mahaifinsa ya garzaya da shi gidan mai maganin gargajiya, wanda ya ce aljanu ne suka shafi Buhari tare da ba shi wasu magunguna.
Sai daga baya makwabtan Adamu suka shaida masa Buhari fa ciwon shan inna (Polio) ne ya same shi, don haka aka kai shi asibiti likitoci suka ba shi taimakon gaggawa, aka yi nasara ya samu sauki.
Shekara biyar bayan nan, Malam Misa yana zaune a karkashin bishiya a kofar gidansa da ke birnin Yola na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya ce ''Lokacin da Buhari ya tashi da safe baya ko iya bude tafin hannunsa.''
A yanzu yana gangamin wayar da kan iyaye kan muhimmancin yi wa yara allurar riga-kafi, inda ya ke taimaka wa jami'an lafiya da ke wannan aiki musamman a yankunan da suke fuskantar tirjiya daga iyaye.
"Na ga amfanin riga-kafi akan dana, don haka duk wanda ya nuna rashin amincewa da ita ina kokarin nuna musu shaida a kai,'' in ji Misa.
Sai dai lamarin ba wai a Najeriya ne kadai ake fuskantar wannan matsala ba. Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce har yanzu iyaye ba sa bayar da hadin kai wajen yi wa 'ya'yansu riga-kafi, kuma matsala ce da ta zama ruwan dare gama duniya.
Misali a wasu kasashen Turai da Amurka da Japan da Indiya kai har da Pakistan har yanzu akwai rashin yadda da yi wa yara allurar riga-kafin cutar Polio.
'Yada jita-jita a kauyuka'
Ma'aikatar lafiya a Najeriya ta ce ya kamata a yi wa yara riga-kafi akalla guda shida na wasu cututtuka a shekarun farko da haihuwarsu ciki har da ta polio, duk yaron da bai samu wadannaa allurai ba to ya na cikin hadari.
Akwai wadatattun alluran riga-kafi a asibitocin birnin Yola wadda za ta wadata a yi wa yara, to amma jami'an lafiya na fuskantar turjiya daga iyaye wadanda ba su aminta da ita ba.
Ana samun rahotannin kai wa jami'an lafiya hari musamman a arewacin Najeriya. Sun yi amanna da cewa akwai wata makarkashiya ta rage yawan al'ummar kasar shi ya sa ake yi wa yara riga-kafin don kashe musu kwayayen haihuwa.
Najeriya na da yawan al'umma miliyan 200, kuma ita ce mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka, sannan kididdiga ta nuna za ta zamo kasa ta uku a duniya mai yawan al'umma nan da shekarar 2050.
Malam Misa ya shaida wa BBC cewa su 13 mahaifinsu ya haifa, kuma ba a yi mu su riga-kafi ba, don haka ya yi tunanin idan har dukkansu sun rayu ba tare da riga-kafi ba, to shi ma nasa 'ya'yan za su rayu.
A yanzu yana da 'ya'ya 10, kuma yana fatan samun karin wasu shida nan gaba, kuma ya yi balaguro a lokacin da aka haifi 'ya'yansa biyu da aka yi musu riga-kafi. Buhari shi ne dansa na uku.
"A lokacin da na dawo daga balaguro, ana ta yada jita-jita a kauyenmu cewa an hada baki da kungiyoyin Turawa da jami'an lafiya da za a yi wa 'ya'yanmu riga-kafi da ke cire wani abu a jijiyar yaranmu, da na ji haka sai na sha alwashin ba zan taba bari a yi wa 'ya'yana ba,' in ji Malam Misa.
'Matakin kashin kai'
Adamu Bawuro sananne ne ga jami'an lafiya saboda kin jinin allurar riga-kafi.
Ya ce babu wani daga cikin 'ya'yansa da aka yi wa riga-kafi, saboda shi ma ba a taba yi masa ba, don haka bai ga dalilin da zai yi wa 'ya'yansa ba.
Hukumar lafiya ta duniya tana daukar hayar mutane don su yi aiki tare da bincike amma me ka iya bincikawa.
Sai dai wani likita a jihar Kogi a arewacin Najeriya, Dr Magnus Ogaraku ya ce ra'ayi kan riga-kafi irin na mutane kamar Bawuro ba su da tushe balle makama.
"Binciken kimiyya ya gano allurar riga-kafi ba ta da hadari, kariya ce daga kamuwa da cutattuka da dama a cikin al'ummarmu.'
Ya amince cewa akwai wasu lokutan da jikin dan adam kan bijirewa riga-kafi har wata ta shigesu, "amma yawancinsu sun taba kamuwa da cutar da ba su san takamaimai abin da ya haddasa ba."
Ana samun kwayar cutar da ke haddasa cutar polio a ruwa maras tsafta da wuraren kazanta.
A wasu yankunan Najeriya, yin bahaya a rafin da ruwan ke gudana da kuma ya ke bi ta ruwan da ake sha na daga cikin abin da ke yada cutar, kuma matukar yaron da ba a yi masa riga-kafi ba ya sha to wannan shi ne mabudin kamuwa da cutar.
Don haka ake karfafawa iyaye gwiwar yi wa 'ya'yansu riga-kafi.
Mecece cutar polio?
- Cutar Polio ko shan inna ta fi kama yara kanana 'yan kasa da shekara biyar
- Cuta ce mai matukar hadari. Tana nannade wasu sassan jiki, takan janyo mutuwar barin jiki ko ma jikin baki daya cikin sa'o'i kadan
- Alamomin kamuwa da cutar sun hada da zazzabi da ciwon kai da amai da ciwon wuya da hakarkari.
- Tana saurin janyo mutuwar jiki, kuma kashi 5 zuwa 10 na yaran kan mutu a lokacin da suka fara samun cushewar numfashi
- A yanzu kasashen Pakistan da Afghanistan ne suka rage a duniya da ke cikin hadarin cutar. Wannan nasara ce idan aka kwatanta da kasashe 125 a shekarar 1988.
Majiya: World Health Organization
Sama da shekara uku kenan ba a samu wanda ya sake kamuwa da cutar polio a Najeriya ba, idan aka ci gaba da tafiya a haka har zuwa badi, to za a ayyanata cikin kasashen da suka yi adabo da cutar.
Sai dai fargabar da jami'an lafiya ke ciki shi ne ta yiwu ba a kai rahoton wadanda suka kamu da cutar zuwa asibiti.
Wani abin damuwa shi ne, yaki da sojin Najeriya ke yi don fatattakar mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, kusa da jihar Adamawa mahaifar Malam Misa mahaifin Buhari, don haka akwai yankunan da jami'an lafiya ba sa iya zuwa don digon riga-kafi ga kananan yara, kamar yadda jami'in Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef, Aliyu Shettima ya shaida wa BBC.
"Ina fatan mu yi nasarar ayyana Najeriya wadda ta kakkabe cutar polio, amma a yankunan da na yi aiki a matsayin jami'in agaji, muna bukatar sake zage damtse a wuraren don tabbatar da cewa polio ba ta bulla ba,' in ji Shettima.
Laureta Anaza na cikin masu bai wa ma'aikatan sa kai horo, wadanda ke shiga kauyuka don yin riga-kafin, ta ce ta yi amanna malaman addinai da sarakunan gargajiya za su iya taka rawa wajen cimma nasara.
Kungiyar da take jagoranta na shiga gida-gida, da taimakon malamai da shugabanni don wayar da kan iyaye kan muhimmancin yi wa 'ya'yansu riga-kafi.
Duk da cewa suna ci gaba da fuskantar tirjiyar iyaye, amma an samu ci gaba matuka idan aka kwatanta da lokutan baya.
Malam Misa ya ce a yanzu ya gane labarinsa da na mahaifinsa sun sha bamban.
"Ina da ilimi da sani kan riga-kafin polio, a yanzu zan iya wayar da kan mutanen da ba su san muhimmancin ta ba," in ji Misa.