Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ana bukatar matakan gaggawa kan sauyin yanayi'
Wani bincike kan sauyin yanayi da masana kimiya 11,000 daga sassan duniya suka amince da shi, ya yi gargadin cewa duniya na fuskantar sauyin yanayi da ke bukatar matakan gaggawa.
Binciken wanda aka yi a kan wasu bayanai na tsawon shekaru 40 ya ce gwamnatocin kasashe sun gaza wajen magance matsalar.
Masanan daga kasashen Amurka da Australia da kuma Afirka ta Kudu da suka gudanar da binciken sun ce, yin gargadin wani hakki ne da ya rataya a wuyansu na sanar da girman barazanar sauyin yanayin da duniya ke fuskanta.
Daya daga cikin masanan, Farfesa Willaim Ripple daga Amurka ya shaida wa BBC dalilin gargadin.
"Ya ce mun fara ganin guguwa mai karfin gaske, da fari da ambaliyar ruwa da kuma tunbatsar teku, don haka muna cikin damuwa cewa wannan somin tabi ne, kuma babu wani mataki da aka dauka kan wannan sauyin yanayin da za a iya magancewa. "
Binciken ya ce akwai alamu masu hatsari kan tasirin sauyin yanayi, wanda ya kunshi karuwar yawan jama'a da karuwar jiragen sama da saran itatuwa. Farfesan ya bayyana abin da ya kamata a yi domin magance matsalar.
"Maimakon kawai magana kan gurbatacciyar iska da ake ta yi, ina ganin ya kamata mu tunkari matsalar sosai, muna tunanin matakai shida da suka shafi dukkanin bangarori na al'umma, ba wai kawai hayaki na masana'antu. Don muna tunani ne kan karuwar yawan jama'a da kuma muhimmacin lura da irin abin da muke ci."
Farfesan ya bayyana fatan cewa za a iya fara ganin sauyi nan ba da dewa ba.
"Za mu gabatar da abin da muka amince kuma yanzu ya rage ga al'umma su yanke hukunci kan matakin da za su dauka, amma dole idan mun kai ga matakin da ya dace domin akwai tattaunawa da dama kan sauyin yanayi kuma muna fatan ganin an fara aiwatar da manufofin."
Masanan dai sun ce dole sai gwamnatocin kasashe sun tashi tsaye domin tunkarar barazanar.