An kori likitoci 77 don sun yi yajin aikin wata 2 kan albashinsu a Zimbabwe

An wallafa

Gwamnatin Zimbabwe ta kori likitoci 77 wadanda suka shafe tsawon watanni byu suna yajin aiki kan kudadensu na albashi.

A watan da ya gabata wata kotu ta zartar da hukuncin cewa yajin aiki ba ya kan doka tare da ba su umurnin su dawo bakin aiki.

Zimbabwe dai na fama da matsalar tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyaki wanda ke tasiri ga rayuwar al'ummar ksar.

Ga alama gwamnatin Zimbabwe za ta ci gaba da tirjiya. Yanzu an kori likitoci 77 kuma akwai sauran abokan aikinsu daruruwa da ke yajin aikin kuma suke jiran sanin makomarsu.

Yana wahala dai a iya daukar matakin korarsu gaba daya domin tuni yajin aikin ya yi tasiri ga harakar kiwon lafiyar kasar.

Saboda tsadar farashin kayayyaki, albashin liktoci bai taka kara ya karya ba, inda albashin likita a Zimbabwe a wata bai kai dala 500 ba.

Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa na ci gaba da fuskantar matsin lamba yayin da al'ummar kasar suka shirya fitowa zanga-zanga a ranar Laraba, a kullum rayuwa kara tsada take ga al'ummar Zimbabewe.