Harin bam ya kashe mutum 13 a Syria

An wallafa

A kalla mutum 13 ne harin bam ya kashe a arewacin Syria. Jami'ai a kasar sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Tal Abyad da ke kusa da kan iyakar kasar.

Ministan tsaron Turkiyya ya bayyana cewa bam din ya fashe ne a cikin wata mota wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutanen 13 tare da raunata a kalla mutum 20.

A watan da ya gabata ne sojojin Turkiyya da kuma 'yan tawayen da Turkiyya ke goya wa baya suka kwace iko da garin na Tal Abyad da kuma wasu garuruwa da ke hannun mayakan Kurdawa, bayan da sojojin Amurka wadanda ke kare mayakan Kurdawan suka janye daga yankin.

Masu goyon bayan sojojin Turkiyya da kuma fararen hula na daga cikin wadanda suka mutu a ranar Asabar, kamar yadda wata kungiya da ke sa ido kan hakkin bil adama a Birtaniya ta bayyana.

Kungiyar ta ce sama da mutum 30 ne suka raunata sakamakon tashin bam din. Ministan tsaron Turkiyya ya zargi mayakan Kurdawa na YPG da dasa bam a cikin motar.

Sai dai babu wata kungiya da ta fito ta dauki nauyin kai harin.

Me Turkiyya ke yi a arewacin Syria?

Sojojin Turkiyya sun kai hari a arewacin Syria jim kadan bayan da sojojin Amurka suka janye daga yankin. Tun can dama akwai rashin jituwa da ta dade tsakanin Turkiyya da Kurdawa inda Turkiyyar ke san korar mayakan Kurdawan daga kan iyakarta da Syria.

Turkiyya na ikirarin mayakan Kurdawa na YPG ''yan ta'adda ne'' wadanda take zargin sun samo asali daga jam'iyyar Kurdawa ta (PKK), wadanda suka gwabza da Turkiyya tun 1984.

Sojojin Turkiyya sun kafa wani babban sansani mai nisan kilomita 120 da suka kira da ''safe zone'' tsakanin garin Tal Abyad da kuma garin Ras al-Ain inda suka fatattaki mayakan Kurdawa daga yankunan.

A ranar Juma'a ne sojojin Turkiyya tare da hadin gwiwar na Rasha suka fara sintiri a yankin.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sha suka a fadin duniya bayan matakin da ya dauka na janye sojojin Amurka daga arewacin Syria wanda hakan ya bai wa Turkiyya damar cin karanta babu babbaka.

Tun a baya dai mayakan Kurdawa da ke a arewacin Syria sun taimaka wa sojojin Amurka wajen yaki da 'yan kungiyar IS, a wannan dalili ne ya sa wasu ke ganin kamar Amurka ta ''ci amanar'' Kurdawa.