Zaben Canada: Trudeau ya sake zama shugaban Canada

Asalin hoton, Cole Burston/Getty Images
Jam'iyyar Justin Trudeau ta Liberal ta sake darewa kan karagar mulki a kasar Canada a karo na biyu, a wani zabe da aka yi wanda ta sha da kyar, sai dai a yanzu zai zama firai ministan gwamnatin 'yan tsiraru ne.
An yi hasashen cewa 'yan jam'iyyarsa za su samu kujeru 157, wato jam'iyya mai rinjaye ta fi su da kujeru 13 ke nan, don haka amincewa da dokoki zai yi musu wuya a karkashin wa'adi na biyu na mulkin Mista Trudeau.
Haka kuma an yi tsammanin 'yan adawa za su samu kuru'u mafiya rinjayen da aka kada, amma hakan bai sa sun samu kujeru a majalisar ba.
An yi zaton za su samu kuri'u 121, wanda ya fi kuri'u 95 da suka samu a baya.
Ko da yake sakamakon da aka fitar a ranar Litinin da daddare ya nuna cewa kujerun jam'iyya mai ra'ayin rikau ta New Democratic Party (NDP), run ragu matuka, amma shugabanta, Jagmeet Singh zai iya zama shi ne ke da karfin fada a ji.
Hasashe ya nuna cewa jam'iyyar NDP za ta samu kujeru 24 ne a cikin kujeru 338 da ke majalisar dokokin kasar.
Jam'iyyar 'yan awaren Quebec ta Bloc Quebecois, wadda ta yi takara ne kawai a wannan lardin ta samu tagomashi, inda ake sa ran za ta samu kujeru 32 idan aka kwatanta da kujeru 10 da ta samu a shekarar 2015.
Kashi 65 cikin dari ne na masu kada kuri'a suka fito suka yi zaben.











