Erdogan ya sha alwashin 'murkushe' mayakan Kurdawa

Reuters

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce kasarsa za ta ''murkushe'' shugabannin mayakan Kurdawa idan har ba su janye mayakansu daga wajen da Turkiyyar ke san kafa sansaninta ba a arewacin Syria.

A ranar Alhamis ne dai Turkiyyar ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki biyar domin bai wa mayakan Kurdawan damar barin yankin.

Sai dai a ranar Asabar, duka bangarorin biyu sun zargi junansu da saba yarjejeniyar.

Turkiyya dai na daukar mayakan Kurdawa a matsayin 'yan ta'adda kuma tana so ta kafa wani sansani da za ta ajiye mayakanta a cikin Syria.

Duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimmawa ta wucin gadi, an ci gaba da tayar da zaune tsaye -- musamman kusa da garin Ras Al-Ain wanda ke kan iyaka.

Me Erdogan ke cewa?

Yayin da Mista Erdogan ke bayani a lokacin wani taro da aka nuna a kafafen talabijin, ya bayyana cewa idan mayakan Kurdawa ba su janye mayakansu ba har zuwa daren talata kamar yadda aka amince a lokacin yarjejeniyar - ''za mu ci gaba daga inda muka tsaya, mu ci gaba da murkushe kawunan 'yan ta'adda.''

Ana sa ran shugaban na Turkiyya zai tattauna da Shugaban Rasha Vladimir Putin a mako mai zuwa. Mista Erdogan ya bayyana cewa idan tattaunawar da za a yi ba ta haifar da wata nasara ba, Turkiyya za ta ''aiwatar da shirinta.''

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta zargi mayakan Kurdawa da kai hare-hare 14 a kasa da awanni 36, akasarin hare-haren a garin Ras Al-Ain.

Ma'ikatar tsaron ta kuma ce Turkiyya tana kiyayye sharudan da aka gindaya lokacin cimma yarjejeniyar.

Sai dai a na su bangaren, mayakan Kurdawan sun zargi gwamnatin Turkiyyar ne da keta yarjejeniyar tsagaita wuta.

Sun kuma zargi sojojin Turkiyya da kin fitar da hanyar da za a ceci farar hula da wadanda suka samu raunuka daga garin da suka kewaye.

A ranar Asabar ne dai mayakan Kurdawan suka bukaci Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence wanda ya taimaka wajen cimma yarjejeniyar da ya matsa wa Turkiyya lamba wajen ganin cewa sun bayar da hanya an fita da fararen hula.