Majalisar Birtaniya za ta kada kuri'a kan Brexit

Asalin hoton, Getty Images
'Yan Majalisar Birtaniya za su kada kuri'ar amincewa da yarjejeniyar Firaminista Boris Johnson ta ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.
Wannan ne karon farko cikin shekara 37 da Majalisar Birtaniya za ta yi zama a ranar Asabar, inda 'yan majalisar za su kada kuri'a kan amincewa da daftarin yarjejeniyar Mista Johnson.
Matakin zai iya ba Birtaniya damar ballewa daga EU a wannan watan ko kuma ya sake jefa kasar cikin wani rudani.
An shafe dare Firaministan kasar na neman goyon bayan 'yan majalisar domin amincewa da yarjejeniyarsa duk da ya nanata cewa ko babu yarjejeniya Birtaniya za ta balle daga EU.
Boris Johnson ya shafe sa'o'i 48 yana kokarin shawo kan 'yan majalisa domin samun goyon bayansu ga yarjejeniyarsa.
Duk da ana ganin lokaci ya kusan kurewa Birtaniya a kuri'ar da 'yan majalisar za su kada domin amincewa ko watsi da yarjejeniyar, amma Mista Johnson ya ce har yanzu yarjejeniyarsa ce mafi dacewar ficewar Birtaniya, tsarin da tun 2016 ya jefa kasar cikin rudanin siyasa.
Mista Johnson ya nanata cewa a karshen wata Birtaniya za ta balle ko da kuwa majalisa ba ta goyi bayansa ba.
A ranar ranar 31 ga wata, wa'adin ficewar Birtaniya ke cika.
Firaminista Johnson yana neman goyon bayan 'yan majalisa 319 daga cikin 650 domin samun tabbacin nasara.
Za a dai shiga tsaka mai wuya idan har aka dage lokacin amincewa da yarjejeniyar, wanda hakan ke nufin neman karin lokaci daga bangaren Tarayyar Turai domin jinkirta ficewar Birtaniya daga EU.
Ana sa ran wasu 'yan Birtaniya za su kaddamar da zanga-zanga a yayin kada kuri'ar domin neman a sake gudanar da zaben raba gardama kan fitar Birtaniya daga EU.

Asalin hoton, Getty Images










