Amurka za ta janye soja 1,000 daga Syria saboda Turkiyya

Wasu abokan huldar Turkiyya a Syria

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Abokan huldar Turkiyya a Syria sai kara samun galaba suke yi
An wallafa

Amurka tana yunkurin janye sojojinta 1,000 daga Arewacin Syria yayin da Turkiyya ke kara matsa kaimin hare-haren da take kai wa Kurdawa, kamar yadda Sakataren Tsaro Mark Esper ya bayyana.

Ya fada wa gidan talabijin na CBS cewa "akwai yiwuwar" Turkiyya za ta fadada hare-haren ba kamar yadda ta tsara ba tun farko.

Turkiyya ta kaddamar da hare-haren ne a makon da ya gabata a yunkurinta na kakkabe mayakan Kurdawa, wadanda abokan huldar Amurka ne, daga garuruwan kan iyaka.

Sama da mutum 130,000 ne suka tsere daga muhallansu da ke kusa da inda ake gwabza yakin, in ji Majalisar Dinkin Duniya.

Ta kuma yi gargadin cewa yawan mutanen zai iya ninkawa har sau uku.

Dakarun kungiyar Syrian Democratic Forces (SDF) wadanda Turkiyya ke kai wa hari, sun yi gargadin cewa ba za su iya ci gaba da tsare mayakan kungiyar IS ba da iyalansu a sansani da kuma gidan yari idan hare-haren suka ci gaba.

A ranar Lahadi ne kuma jami'an Kurdawa suka bayyana cewa 'yan uwan mayakan IS din kusan 800 ne suka tsere daga sansanin Ain Issa yayin da ake ci gaba da fafatawa.

Mece ce hikimar daukar matakin?

Yanayi a Syria na kara "tabarbarewa", Sakataren Tsaron Amurka Mark Esper ya bayyana a ranar Lahadi.

"A cikin sa'a 24 da suka wuce mun fahimci cewa Turkiyya ka iya fadada hare-haren zuwa kudanci da kuma yammaci sama da abin da ta tsara tun farko."

Ya kara da cewa matakin janye sojojin ya biyo bayan tattaunawa ne da masu fada-a-ji kan tsaron kasa da kuma Shugaba Donald Trump.