An kashe jagora a kungiyar al-Qaeda

Asalin hoton, NDS Afghanistan
An kashe daya daga cikin shugabannin kungiyar al-Qaeda a wani samame da sojojin hadin gwiwa na Amurka da na Afghanistan suka kai a watan da ya gabata, inji hukumar tattara bayanan sirri ta Afghanistan.
Asim Umar, wanda shi ne shugaban kungiyar a yankin kudancin nahiyar Asiya, an kashe shi a samamen da aka kai a wani gida na 'yan kungiyar Taliban a lardin Helmand a ranar 23 ga watan Satumba.
An bayyana cewa a samamen, a kalla fararen hula 40 ne suka rasa rayukansu.
Sai dai kungiyar al-Qaeda da kuma Amurka ba su tabbatar da mutuwar Umar ba.
Hukumar tattara bayanan sirri ta Afghanistan, a sanarwar da ta wallafa ta mutuwar Umar, ta kuma wallafa hotuna da ke nuna Umar a lokacin yana da rai da kuma bayan mutuwarsa.
Sai dai ba ta bayyana sauran bayanai dangane da yadda aka yi da gawarwakin wadanda suka mutun ba.
Ganin daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar al-Qaeda da aka yi a gidan 'yan Taliban ya sa mutane sun fara tambayoyi ko kuma nuna shakku kan niyyar kungiyar 'yan tayar da kayar bayan ta yanke hulda da masu ikirarin jihadi a matsayin daya daga cikin yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka.
Amurka ta fara yakar Afghanistan a 2011 bayan harin da aka kai na 9 ga watan Satumbar 2001, wanda aka fi sani da 9/11 sakamakon 'yan kungiyar Taliban wadanda ke mulkin kasar a wancan lokaci sun ki mika Osama bin Laden ga Amurkar.
Kafin Shugaba Donald Trump na Amurka ya fita daga yarjejeniyar zaman lafiya a watan da ya gabata, Amurkar da Taliban sun kusan cimma matsaya wacce za ta haifar da Amurkar ta janye dakarunta a matsayin musaya da kungiyar Taliban ta daina duk wani kawance da kungiyar al-Qaeda.
Kungiyar Taliban dai ta dade tana yaki da gwamnatin Afghanistan da kuma sojojin wasu kasashe tun bayan da Amurka ta afka mata a 2001 inda take da iko da sassa da dama na kasar.

Asalin hoton, EPA
Jami'ai a Helmand sun tabbatar da cewa samamen da sojojin suka kai ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama a wajen biki.
Jami'ai a Amurka sun bayyana cewa suna bincike kan rahoton da aka fitar na mutuwar fararen hula da dama.
Sai dai jami'an sun bayyana cewa akasarin wadanda suka mutu sun mutu ne sakamakon bam da 'yan kunar bakin wake suka tayar.
Amurka da Afghanistan sun zargi 'yan kungiyar Taliban da amfani da fararen hula a matsayin Garkuwa.
Kafar yada labarai ta CBS ta ruwaito cewa akwai jami'an sojojin Amurka na musamman a samamen da aka kai.
Umar ya shugabanci kungiyar al-Qaeda a Indiya da yankunan da ke makwabtaka da ita tun Satumbar 2014.











