Taraba: Dalilan da suka jawo kashe 'yan sandan IRT

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar sojojin Najeriya ta ce karancin bayanai da kuma rashin yin aiki tare ne dalilan da suka jawo kisan 'yan sandan nan uku da sojoji suka yi tare da fararen hula biyu a jihar Taraba ranar 6 ga watan Agusta.

Sanarwar na kunshe ne a wani bayani da ta wallafa na sakamakon binciken da wani kwamiti ya mika, wanda Hafsan Hafsoshin Najeriya Janar Abayomi Gabriel Olonisakin ya kafa bisa umarnin Shugaba Muhammadu Buhari.

Kwamitin mai mambobi bakwai wanda Admiral Ibikunle Taiwo Olaiya ya jagoranta, ya kunshi wakilai daga rundunar sojan kasa da ta ruwa da ta sama da hukumar tattara bayanan sirri ta Najeriya da rundunar 'yan sanda da kuma ta farin kaya wato SSS.

"Bayan wani bincike cikin tsanaki, kwamitin jin bahasin ya bayyana cewa an samu rashin bin doka tare da rashin tuntuba tsakanin dakarun sojoji da na 'yan sanda," kwamitin ya bayyana a sanarwar.

Ya kara da cewa: "Kazalika duka bangarorin biyu ba su bi dokar tsarin aiwatar da ayyuka ba ta Standard Operating Procedure sannan ya bayar da wasu shawarwari ga bangarorin.

"Ya kamata rundunar soja ta binciki Kyaftin Tijani Balarabe da Saja Ibrahim Mohammed da Kofur Bartholomew Obanye da DCO na ofishin 'yan sanda na Ibi da ASP Aondoona Iorbee da Insifeto Aliyu Dadje bisa samun hannunsu a ciki.

"Kwamitin kuma ya bayar da shawarar sake bincikar Hamisu Bala Wadume bisa zargin fasa kwaurin bindigogi zuwa Najeriya."

A karshe kwamitin ya ce ya kamata rundunonin biyu su kafa cibiyar yin aiki tare wacce za ta hada manyan jami'ansu domin guje wa faruwar hakan nan gaba.