Jirgin sama ya fada kan wani gida a Afirka ta Kudu

An wallafa

'Yan sandan Afirka ta Kudu sun ce wani matukin jirgin sama dan shekara 30 a duniya ya mutu yayin da fasinja daya ya jikkata bayan jirgin ya fada kan garejin wani gida a Arewa maso Yammacin kasar.

An kwantar da fasinjan a wani asibiti bayan hatsarin jirgin a lardin Huhudi, mai nisan kilomita 400 daga Johannesburg, babban birnin kasar.

Rundunar 'yan sandan kasar ta ce tana gudanar da bincike kan lamarin da take yi wa kallo a matsayin kisan kai.

Har yanzu ba a san dalilin hatsarin jirgin ba.