Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Paul Biya ya ba da umarnin sakin fursina 333 a Kamaru
Shugaban Kamaru Paul Biya ya bayar da umarnin sakin fursina 333 wadanda aka tsare saboda zarginsu da alaka da masu fafutikar ballewa daga kasar.
Wata sanarwa daga fadar shugaban ta ce an fasa gurfunar da mutanen a gaban kotun soji.
Wani jami'in gwamnatin Kamaru ya bayyana a wajen wani taron manema labarai cewa suna kokarin sulhu bayan kwashe shekara uku ana rikicin da ya yi ajalin dubban mutane da kuma raba kimanin mutum 500,000 da muhallinsu.
Rikicin ya fara ne a lokacin da wasu lauyoyi da malamai suka fara yajin aiki dangane da amfani da Turancin Faransa a kotuna da makarantu a yankin da ke magana da Turancin Inglishi a yankunan Arewa-maso-Yammaci da kuma Kudu-maso-Yammacin kasar.
A watan Oktoban 2017, masu fafutika sun ayyana samun wani kwarya-kwaryar 'yanci a yankunan biyu - wani abu da Shugaba Biya ya yi watsi da shi.
Daga nan ne wasu daga cikin masu fafutikar suka dauki makamai, abin da ya jawo arangama tsakaninsu da dakarun gwamnati.
Sai dai ba a san ko umarnin sakin fursinonin zai bayar da damar sakin manyan jagororin 'yan awaren ba.
Akwai masu sharhi da ke ganin da wuya 'yan awaren su yi maraba da sakin fursinonin - wadanda suka kafe wajen ganin sun kafa kasar Ambazonia daga kasar Kamaru.