Buhari zai kai ziyara Afirka ta Kudu

An wallafa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara kasar Afirka ta Kudu a ranar Laraba, bayan wata gayyata da Shugaba Cyril Ramaphosa ya aika masa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa shugabannnin za su tattauna batutuwa ne da suka shafi walwalar 'yan Najeriya.

Haka zalika za su duba batun yadda za a gyara dangantakar da ta yi tsami tsakanin kasashen biyu.

Wannan ziyarar tana zuwa ne makonni kadan bayan wasu jerin hare-haren kin jinin baki da wasu 'yan Afirka ta Kudu suka rika kai wa baki 'yan kasashen waje ciki har da 'yan Najeriya.

Abin da ya jawo dawo da daruruwan 'yan Najeriya gida daga Afirka ta Kudu.

Yayin ziyarar, an shirya Shugaba Buhari zai yi wata tattaunawar musamman da 'yan Najeriya mazauna Afrika ta Kudu, kamar yadda Garba Shehu ya ce.

Ana saran Shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya ne a ranar Juma'a.

A hukumance gwamnatin Afirka ta Kudu ta nemi afuwar Najeriya kan tashin hankalin da ya faru.

Najeriya da Afirka ta Kudu su ne manyan kasashe mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.