Tankar mai ta yi taho-mu-gama da Golf a Zamfara

Zamfara map
An wallafa

Rahotanni daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa an yi wani mummunan hatsarin mota da ake tunanin mutane da dama sun mutu.

Wani wanda abin ya faru a gabansa Nasiru Aliyu Bukkuyum ya shaida wa BBC cewa motar dakon mai ce da ta fito daga Funtua ta yi taho mu gama da wata motar fasinja kirar Golf.

"Motar ta wuce garin Damba da kadan kenan sai wannan abu ya faru, amma dai ba mu san adadin mutanen da suka mutu ba, sai dai tabbas an samu asarar rayuka.

Lamarin dai ya faru ne da safiyar Juma'a. Sai dai zuwa yanzu BBC ba ta ji ta bakin hukumomi ba kan hatsarin.

A lokacin da abokin aikunmu Muhammad Annur Muhammad ke magana da wadanda abin ya faru a kan idonsu ta wayar tarho, ya ringa jin jiniyar motar kashe gobara da ta agaji.

Yaron tankar da ya samu tsira, wanda kuma ya kasance da ne ga direban tankar ya shaida wa BBC cewa "Babana ne ke jan motar kawai sai mai Golf ta fasinja ya zo ya yi mana overtaking, hakan ya sa kan motar ya kufcewa mahaifina.

"Daga nan sai motarmu ta kife, sai ta kama da wuta. To dama mu uku ne a ickinta, mu biyun muntsira amma shi mahaifina da yake ta bangarensa motar ta kife bai samu fitowa ba.

"Ni dai na tabbatar ya mutu saboda ai motar ta riga ta kone kurmus," a cewar yaron motar.

Ya kara da cewa ga dukkan alamu su ma mutanen da ke cikin Gof din babu wanda ya tsira.

Tankar da ta fadi din dai yaron motar ya ce ta kamfanin Ataf Oil ce.

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

Hatsarin manyan motocin dakon mai na neman zama ruwan dare a Najeriya, kuma ana ganin hakan na yawan faruwa ne saboda rashin kyawun tituna da kuma rashin sanya dokokin da za su hana manyan motoci yawo da rana ko kamar yadda ake yi a wasu kasashen da suka ci gaba.

Ko a wannan shekara da muke ciki ta 2019 an samu hadurra na motocin dakon mai a wasu sassa na kasar.

Kuma hakan na ci gaba da zama silar mutuwar 'yan Najeriya da dama.

A watan Yulin 2019 ma lokacin da irin wannann hadarin ya afku, wani jami'i a hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC Muhammad Kabir Abubakar, ya ce 'yan Najeriya fiye da mutum 600 ne suka mutu a shekaru biyu da suka gabata sakamakon hadarin motocin dakon mai.

Ya ce mutum 302 ne suka mutu a 2018, inda mutum 308 suka mutu a shekara 2017 sakamakon hadurran motocin dakon mai.

Muhammad Kabir Abubakar ya danganta irin wannan hadari da dalilai guda uku kamar haka:

  • Aiki fiye da kima da ke sa direbobin kwashe kwanaki suna aiki ba tare da sun runtsa idanunsu ba
  • Shan kayan maye da na kara kuzari
  • Tukin ganganci.

Jami'in hukumar FRSC din ya nuna irin yadda wasu mutanan da ba su ji ba su gani ba ke mutuwa sakamakon hadarin motocin, inda a wasu lokutan wuta ke tashi ta kone gidaje da mutane.