Sojoji sun sake rufe ofishin kungiyar agaji a Najeriya

An wallafa

Hukumomi a Najeriya sun dakatar da ayyukan kungiyar bayar da agaji ta Mercy Corp a jihohi biyu na arewa maso gabashin kasar.

Wasu bayanai na cewa an dauki matakin ne bayan da sojoji suka kama wani mutum dauke da makudan kudade, wadanda ya ce mallakin kungiyar ne, abin da a ya zamo abin zargi daga bangaren hukumomi.

Ko a makon da ya gabata dai rundunar sojin kasar ta dakatar da ayyukan kungiyar Action Against hunger wadda ta zarga da taimaka wa mayakan kungiyar Boko Haram, abin da kungiyar ta musanta.

Rufe ayyukan kungiyar ta Mercy Corp na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ganin sauye-sauye daga rundunar Lafiya Dole mai yaki da kungiyar Boko Haram a arewa-maso-gabashin Najeriya.

Kungiyar dai ta ce ta dakatar da ayyukan nata ne a jihohin Borno da Yobe bayan da sojoji suka rufe ofisoshin nata guda biyu a yankin ranar Laraba.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta hannun shugabanta mai kula da sadarwa da yada labaru, Amy Fairbairn, ta ce babu wani karin bayani ko kuma dalili da hukumomi a kasar suka bayar game da rufe ofisoshin.

Sai dai kungiyar ta ce za ta so ta yi aiki tare da sojojin domin ganin an shawo kan ko ma wace irin matsala ce ta haifar da hakan.

Duk da haka kungiyar ba ta yi karin bayani game da ko zuwa yaushe ne wannan dakatarwa za ta kare ba.

A bangare guda kuma rundunar lafiya Dole ta tabbatar da cewa an rufe ofisoshin kungiyar, tare da dakatar da ayyukanta.

A tattaunawar da BBC ta yi da shugaban rundunar, Birgediya Olusegun Adeniyi, ya ce duk da ba ya son yin dogon bayani game da lamarin to amma zai iya tabbatar da dakatar da ayyukan kungiyar.

Sai dai ya ce za su fitar da karin bayani a cikin takardar da za su fitar ga manema labarai ta hannun jami'insu mai kula da bangaren yada labaru na rundunar.

Kafofin yada labaru da dama sun ruwaito cewa bayanai da aka samu wadanda ba na hukuma ba daga rundunar na nuna cewa an dakatar da ayyukan hukumar ne bayan da jami'an soji suka kama wani mutum dauke da kudi dala miliyan 29, wadanda aka alakanta da kungiyar.

Kungiyar dai na ikirarin cewa tana aiki ne a yankin domin bayar da agaji ga mutanen da ke cikin mawuyacin hali a yankunan Najeriya da ke fama da rikici.