Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Boeing zai biya diyyar $50m ga iyalan wadanda suka mutu
Kamfanin kera jiragen sama na Boeing ya sanar da cewa zai biya iyalan wadanda suka mutu a hatsarin jirgin Ethiopia samfurin Boeing 737 Max diyyar $144,500 kwatankwacin naira miliyan 52 ga kowane mutum daya.
Kudin zai fito ne daga wani asusun tallafi na dala miliyan 50 wanda Boeing ya sanar da kafa shi a watan Yuli.
Asusun ya fara shirye-shiryen biyan iyalan wadanda suka rasa rayukansu kuma za a kammala shirye-shiryen kafin shekarar 2020.
Lauyoyin iyalan, wanda mafi yawansu sun kai kamfanin kotu sun yi watsi da kafa asusun inda suka ce farfaganda ce.
"Dala 144,000 ba ta isa ta share hawayen wadannan iyalan ba," inji Nomaan Husain, wani lauya a garin Texas da ke wakiltar iyalai 15 a kotu.
"Wannan ba abu ne da zai gamsar da wadannan iyalai ba. Iyalan nan na bukatar su san gaskiyar abin da ya faru."
Daukar hankali?
Tun a watan Maris ne dai aka dakatar da amfani da 737 Max, yayin da masu bincike ke tantance amincin jirgin bayan hadurran da ya yi a Indosiya da Habasha, inda sama da mutane 340 suka mutu.
A watan Yuli ne kuma Boeing ya yi alkawarin biyan dala miliyan 100 ga iyalan al'umomin da hadarin ya shafa.
Daga baya kamfanin ya ce zai ware rabin kudin don biyan iyalan wadanda suka mutu diyya yayin da za a yi amfani da sauran rabin wajen samar da ilimi da cigaban yankunan da hadarin ya shafa.
Robert A Clifford shugaban lauyoyin Ethiopian Airlines ya ce rashin bayanai a lokacin da aka fara yin sanarwar ya nuna cewa Boeing ya yi amfani da damar wajen dauke hankalin jama'a daga yin tambayoyin da suka dace.
Da yawa daga cikin 'yan uwan wadanda suka mutu dai na so a gina wuraren tunawa da 'yan uwansu, sannna suna ci gaba da tambayar yadda kamfanin Boeing ya ke so ya kashe ragowar dala miliyan 50 din.
"Abin tashin hankali guda dangane da hatsarin jirgi shi ne iyalan wadanda suka mutu ba sa samun wani abu a madadin 'yan uwansu," a cewarsa.
'Mataki mai muhimmanci'
A wata sanarwa, Shugaban Boeing Dennis Muilenberg ya bayyana bude asusun a matsayin wani mataki mai muhimmanci a kokarin kamfanin na taimakon dangin mutanen da suka mutu a hatsarin Boeing 737 Max 8.
Shiga shirye-shiryen asusun dai na radin kai ne.
Ba lallai ne iyalan da suka shigar da bayanansu don karbar diyya su ki shigar da kara kotu ba, in ji Kenneth Feinberg, jami'in kula da asusun, wanda kuma shi ne ya sa ido kan rarraba kudin diyya ga wadanda hare-haren Amurka na Satumba 11 ya shafa.