Zanga-zangar kin jinin al-Sisi ta barke a Masar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

An yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da ba a taba ganin irin ta ba tun bayan hawan shugaba al-Sisi karagar mulki a shekarar 2014.

Dubban Masarawa ne suka cika dandalin Tahrir a birnin Alkhahira, wurin da aka fara juyin juya halin kadawar guguwar sauyi a shekarar 2011.

Rahotanni sun bayyana cewa ana gudanar da irin wannan zanga-zanga a wasu biranen kasar.

Masu boren dai na korafin yadda cin hanci da rashawa ya mamaye gwamnatin al-Sisi kuma ba ya daukar matakan da suka dace.

Wani dan kasuwa kuma mai shirya fina-finai Muhammad Ali, ya wallafa wasu bidiyo shafin internet ya na zargin shugaban da kashe miliyoyin daloli wajen siyen gidajen alfarma, da otal-otal ya yin da miliyoyin 'yan Masar ke rayuwa cikin tsananin talauci. Sannan matakin tsuke bakin aljihu da nufin farfado da tattalin arzikin kasar da gwamnati ta dauka shi ma ya kara jefa Masar cikin halin ni 'ya su.

Sai dai shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya musanta zargen-zargen inda ya kira su na karya tsagwaronta.

Me ke faruwa ne a kasar Masar?

Tun a ranar juma'a ne 'yan kasar suka fara wallafa wasu kalamai a shafin Twitter, "Sisi ka sauka daga mukami" da "Jama'a na son hambarar da wannan mulkin", wadannan su ne kalaman da ke cin kasuwa tun da safe a kasar Masar.

Masu boren sun yi fitar dango, tare da cika dandalin Taharir, duk kuwa da cewa an yi ta amfani da hayaki mai sa hawaye dan tarwatsa su.

Wakilin BBC a Masar ya wallafa a shafinsa na Twitter, kwanaki kadan da suka gabata idan aka ce hakan za ta afru ba lallai ne a yadda ba.

Kafar yada labaran Al Jazeera, ta rawaito zanga-zanga irin wannan ta barke a birni na biyu mafi girma a kasar wato Al-askandariyya.

A ranar 2 ga watannan ne Mista Ali da ke gudun hijira a kasar Spain, ya fara wallafa Bidiyon sukar gwamnatin Masar. A wani bidiyon da ya wallafa a ranar Talata, Mista Ali ya ce idan zuwa ranar alhamis shugaba al-Sisis bai sauka daga mukami ba, to 'yan kasar za su fito zanga-zanga dandalin Taharir a ranar juma'a.

A shekarar 2013 ne, Abdel Fattah al-Sisi ya jagoranci sojin Masar suka hambarar da gwamnatin shugaba na farko da aka zaba a tsarin dimukradiyya marigayi Muhammad morsi, bayan zanga-zangar kin mulkinsa.

Tun daga lokacin kungiyoyin kare hakkin dan adam ke zargin gwamnati da take hakkin jama'a, da kame dubban 'yan adawa ciki har da tsare marigayi Morsi wanda a shekarar nan ya rasu a kotu a ranar da ake zaman sauraron karar da ake masa.

A kuma watan Afirilu ne aka kada kuri'ar amincewa da yi wa kundin tsarin mulkin Masar garanbawul, inda ya bai wa shugaba Abdel Fattah al-Sisi damar zama shugaban kasar har zuwa shekarar 2030.