Sudan ta Kudu: Yaki ka iya dawowa in ji kwararru

An wallafa

Tawagar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a dakile bangarorin siyasa masu tsattsauran ra'ayi a Sudan ta Kudu daga jefa kasar cikin yaki.

Kwararrun sun ce matukar aka bari 'yan siyasar suka kawo wa yarjejeniyar da aka kulla a bara cikas, to Sudan ta kudu na iya komawa cikin yaki tsundum.

"Manyan 'yan siyasar Sudan ta Kudu na amfani da matsananciyar wahalar da mutanen kasar ke ciki wajen biyan bukatunsu," inji shugabar hukumar kare hakkin dan Adama ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu, Yasmin Sooka.

A takardar da ta gabatar a madadin hukumar, Yasmin Sooka ta ce tawagarta ba ta jima da dawowa daga Sudan ta Kudun ba, inda suka gano yawancin 'yan kasar na fama yunwa a kullum.

"Da gangan aka kirkiro yunwar da ake fama da ita a kasar... daga cikin dabarun da bangarorin masu yakar juna a kasar ke amfani da su a kan fararen hula, wanda hakan laifi ne na yaki.

"Babu tamtama bangarorin siyasa masu gaba da juna a kasar na da hannu a matsalar bukatun ababen more rayuwa da ake fama da ita a kasar."

Ta kafa da cewa hukumar na maraba da tattaunawar da aka yi tsakanin shugaba Salva Kiir da madugun 'yan adawa Riek Machar, inda suka kulla yarjejeniyar kafa gwamantin hadin gwiwa a watan Nuwamba.

Ta yi bayanin cewa akwai masu tsattsauran ra'ayin siyasa da ba sa so su hakura da wasu batutuwa da za a daidaita a kai, ciki har da batun yawan jihohi da iyakokin jihohin da kuma matakan tsaro.

Hakan a cewarta na iya kawo cikas ga nasarar da aka samu wajen aiwatar da yarjeniyar.

Domin haka ta bukaci jami'an hukumar da su matsa wa shugabannin lamba, domin tabbatar da kafa gwamnatin hadin gwiwa a kasar, inda yakin basasa ya tilasta wa kusan mutum miliyan hudu rabuwa da gidajensu.

Matakan da take ganin ya kamata a dauka a nan gaba sun hada da biyan diyya da tallafa wa mutanen da yakin basasar ya shafa, a cewarta.

Sooka ta kuma bayar da shawarar ware kashi daya cikin dari na kudaden man kasar domin yin hakan, maimakon karkatar da su da 'yan siyasa ke yi, kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Ta ce kasashen nahiyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya na da ikon sa hakan ta faru.