Zirin Gaza: Harin kunar bakin wake ya kashe 'yan sanda uku

An wallafa

Wasu 'yan kunar bakin wake da ke da alaka da kungiyar Islamic State (IS) sun kai hari kan wasu wuraren da ake duba motoci a Gaza, wanda yayi sanadin mutuwar 'yan sandan Falasdinu uku.

Hare-haren sun biyo bayan wani samame da Hamas ta kai kan mayaka masu alaka da IS a yankin na Gaza wanda ta ke iko da shi.

Jami'an tsaron Zirin Gaza har sun taba tsare daya daga maharan da suka kai hare-haren na ranar Talata.

Tuni kungiyar Hamas mai iko da Zirin ta kafa dokar ta baci a fadin yankin.

An kashe jami'an 'yan sanda biyu yayin harin da aka kai na farko, ban da raunata wani dan sandan daya, kuma maharin wanda ya kai harin ne a shingen duba ababen hawa da jami'an tsaro suka kafa.

Hari na biyu ya biyo bayan na farko ne kasa da sa'a guda kuma ya kashe wani dan sanda daya, bayan raunata wasu mutanen da ba a san adadinsu ba a wani wurin duba ababen hawa na daban.

An dai baza daruruwan jami'an tsaro a bisa titunan Zirin Gaza bayan hare-haren.

Kungiyar Hamas ta sha fuskantar hare-hare irin wadannan daga masu biyayya ga kungiyoyi kamar IS, kuma ba ta dade da sakin wasu 'ya'yan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi da ta ke tsare da su ba domin sasanta tsakanin al'umomin yankin.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2007 ne kungiyar Hamas ta kwace ikon gudanar da Zirin na Gaza daga Hukumar Falasdinawa karkashin Shugaba Mahmoud Abbas.